Dukkan Kabilun Kasar Sin Na Zaman Tsintsiya Madaurinki Daya
Bayan shafe tsawon shekaru 105 da kafuwar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin da yadda gwamnati karkashin jam’iyyar ke ci gaba da jagorantar kasar Sin cikin hikima da hangen nesa da tarin nasarori, ba na zaton akwai wani abu da gwamnati za ta bullo da shi, da zai sa a ga baikenta kamar yadda wasu suke yi. Salon shugabanci da nasarorin da kasar Sin ta samu cikin gomman shekaru, ya nuna mana cewa, gwamnatin kasa ce kadai ke da alhakin tafiyar da harkokinta yadda ya dace da yanayi da jama’arta, kuma ita ce ta fi kowa sanin abun da ya dace da al’ummarta. Yadda wasu kasashen yamma da kafafensu na yada labarai ke kokarin jirkitawa da yada jita-jita game da sabuwar dokar kasar Sin dake nufin kara tabbatar da dunkule dukkan kabilun kasar wuri guda, abun mamaki ne matuka. Manufar dokar dai ita ce karfafa hadin kan kasa da tabbatar da daidaito da kuma inganta mu’amala tsakanin kabilu daban-daban. Duk wanda ke bibiya ko ya ziyarta ko yake zaune a kasar Sin kamar ni, to tabbas ya san yadda gwamnatin kasar ke mayar da hankali kan dukkan al’ummominta ba tare da wariya ko son kai ba, don haka me ya sa za ta fitar da dokar da za ta nuna wariya ko musgunawa jama’arta? Daya daga cikin abubuwan da suka haifar da hadin kai da ci gaban al’ummar kasar Sin shi ne, sanin cewa dukkansu Sinawa, ’yan uwan juna, kuma tsintsiya madaurinki daya, kishin kasarsu na gaba da komai. Kuma wannan kishin da suke da shi a zukatansu ne, kashin bayan ci gaban da suke samu a kai a kai kuma na ban mamaki. A tunanina, masu fassara wannan doka ta bahaguwar hanya, na yi ne domin cimma wata manufa tasu, ko kuma son ganin al’ummomin kasar sun fada cikin matsalar rarrabuwar kawuna kamar yadda suke ciki, abun da na yi imanin kasar Sin ba za ta taba bari ba. (Fa’iza Mustapha)



















