Jimillar Cinikayyar Lantarki Ta Karu Da 19.2% Cikin Farkon Watanni 8 A Sin
Bayanin da hukumar makamashin kasar Sin ta fidda, ya nuna cewa, a tsakanin watan Janairu zuwa watan Agustan bana, yawan...
Bayanin da hukumar makamashin kasar Sin ta fidda, ya nuna cewa, a tsakanin watan Janairu zuwa watan Agustan bana, yawan...
Da yammacin yau Talata 22 ga watan Satumba, firaministan kasar Sin, Li Qiang, ya gana da Francis Hourant, shugaban kungiyar sana’o’in fasaha ta kasa da kasa, da David Hoey, babban jami’in gudanarwarta a birnin Shanghai, wadanda suka zo kasar Sin domin halartar gasar sana’o’in fasaha ta kasa da kasa karo na 48. Li Qiang ya bayyana cewa, kasar Sin na da kwarin gwiwar yin aiki tare da dukkan bangarori domin gabatar wa duniya wani babban bikin sana’o’in fasaha na musamman. Kasar Sin a shirye take ta kara zurfafa hadin gwiwa da kungiyar sana’o’in fasahar, da yin hadin gwiwar zurfafa ci gaban fannin sana’o’in fasaha a duniya, da bunkasa tattalin arzikin duniya mai dorewa cikin kwanciyar hankali, kana da kyautata jin dadin al’ummomin dukkan kasashe. Za a gudanar da gasar sana’o’in fasaha ta kasa da kasa karo na 48 ne a birnin Shanghai daga ranar 22 zuwa 27 ga watan Satumba, yayin da za a gudanar da bikin baje kolin kasuwancin fasahohin zamani na duniya karo na biyar a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang, daga ranar 23 zuwa 27 ga watan Satumba. Bisa gayyatar kasar Sin, firaministan kasar Malaysia, Anwar Ibrahim, zai halarci bikin bude gasar ta sana’o’in fasaha ta kasa da kasa da kuma bikin kaddamar da baje kolin kasuwancin fasahohin zamani na duniya. Bugu da kari, shugaban majalisar ministocin kasar Kyrgyzstan, Adylbek Aleshovich Kasymaliev, zai halarci bikin kaddamar da baje kolin kasuwancin fasahohin zamanin na duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Ma’aikatar raya masana’antu da fasahohin sadarwa ta kasar Sin, ta ce gwamnatin kasar ta sha alwashin zakulowa, da tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu da ake da kyakkyawan fatan bunkasarsu. Ma’aikatar ta ce maimakon jiran har sai irin wadannan masana’antu sun nuna bukatarsu ta neman taimako, gwamnati za ta himmatu wajen lalubo su da tallafa musu yadda ya kamata. Karkashin hakan, ma’aikatar za ta kyautata tsarin tallafinta ga irin wadannan masana’antu, musamman masu amfani da fasahohin zamani da kwarewa, ta yadda za su kai ga sarrafa hajoji masu kima da fice tsakanin nau’o’insu, kana za a matsa kaimi wajen lalubo sabbin kamfanoni da ake ganin za su ciri tuta a nan gaba, musamman ma wadanda ke mayar da hankali ga ayyuka masu kunshe da fasahohin kirkire-kirkire, da masu bunkasa sabbin hajoji. A jiya Lahadi ne ma’aikatar ta alkawarta hakan, yayin wani taron masu ruwa da tsaki, yayin tattaunawa dangane da hanyoyin kyautata tsarin bincikowa, da samar da karin hidimomi ga irin wadannan masana’antu. Wani jami’in ma’aikatar ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da inganta tsarin shari’a da manufofin gudanarwa, da shirye-shiryen kyakkyashe masana’antu, da tallafawa ’yan kasuwa da hidimomi ta yadda za a kai ga ingiza ci gaba mai nagarta tsakanin kanana da matsakaitan masana’antu. Kazalika, za a ci gaba da karfafa gwiwar kamfanoni ta yadda za su kai ga cimma muradun kwarewa, da ci gaban kirkire-kirkire, da fadada bincike da samar da ci gaban harkokin zuba jari, da kokarin cimma sabbin nasarori a muhimman fasahohi. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta Sin, Guo Jiakun, ya bayyana a yau Litinin cewa, a ranar 25...
Rahoton baya bayan nan mai taken "Rahoton cinikayyar hajojin dakile sauyin yanayi na Sin na 2026", ya bayyana yadda darajar...
A kwanan nan, shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya mayar da amsa ga dalibai daga jami’o’in Amurka guda 10, wadanda...
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping zai je ziyarar aiki a Amurka daga ranar 23 zuwa 25 ga watan Satumba bisa...
Cibiyar lura da ayyukan ‘yan sama jannati ta kasar Sin, ta ce kasar ta yi nasarar noma sama da nau’o’in...
A rana ta farko ta fafata gasar wasannin motsa jiki ta nahiyar Asiya karo na 20 da ke gudana a...
A yau Lahadi, kasar Sin ta aike da taurarin dan’adam guda tara zuwa sararin samaniya ta hanyar amfani da rokar...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.