Sin Ta Gina Cibiyoyin Luban 38 A Kasashe 32
A shekarun baya-bayan nan, tsarin ba da ilmi kan sana’o’i na Sin ya samu sabon ci gaba, kuma ya zama sabon karfi na hadin gwiwa wajen ba da ilimi na kasa da kasa. Cibiyoyin Luban cibiyoyi ne da ke samar da ilimi na digiri ko horar da ma’aikata sana’o’i, wadanda jami’o’in Sin ke gudanarwa a ketare da hadin gwiwar wasu kasashe. Ya zuwa yanzu, an gina cibiyoyin Luban 38 a kasashe 32, inda aka horar da dalibai a matakin digiri sama da dubu 30, kuma yawan dalibai da ba na matakin digiri ba da aka horar ya haura dubu 160. A wani bangare na daban kuwa, ma’aikatar ba da ilimi ta kasar Sin na aiwatar da ayyukan ba da ilimi kan sana’o’i sama da 500 cikin hadin gwiwa a kasashe da yankuna sama da 80, matakin dake taka rawar gani wajen horar da ma’aikata kwararru, a bangaren hadin gwiwar karfin samar da abubuwa da hidimomi a kasa da kasa, da kuma tallafa wa kamfanonin Sin wajen habaka hadin gwiwarsu da kasashen waje. (Amina Xu)



















