Peng Liyuan Ta Gabatar Da Jawabi Ta Faifan Bidiyo A Bikin Samar Da Lambar Yabo Kan Aikin Ilmantar Da ’Ya’ya Mata Na UNESCO Na Shekarar 2026
An gudanar da bikin samar da lambar yabo ga aikin ilmantar da ’ya’ya mata na UNESCO na shekarar 2026 a birnin Paris na Faransa jiya Juma’a. farfesa Peng Liyuan, uwar gidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma wakiliyar musamman ta UNESCO kan ingiza aikin ilmantar da ’ya’ya mata, ta aika da jawabi ta faifan bidiyo zuwa bikin, don taya murna. A jawabinta farfesa Peng Liyuan ta nuna cewa, Sin ta dade tana mai da hankali sosai kan ba da ilmi ga ’ya’ya mata, kuma tana hadin gwiwa da UNESCO da sauran bangarorin da abin ya shafa tare da samun ci gaba a zo a gani, wanda ya amfani mata da dama a kasashe da yawa. A shekarun baya-bayan nan, Sin ta yi amfani da fasahar AI don karfafa karfin ba da ingantaccen ilmi, wanda hakan ya taimaka sosai wajen ingiza daidaito tsakanin jinsi a fannin ba da ilimi da inganta rayuwar mata gaba daya, kuma ta more dabarunta ga kasashe masu tasowa. A cewarta, ana dora nauyi sosai a kan aikin ba da ilmi ga ’yan mata da mata a cikin dogon lokaci. A matsayinta na wakiliyar musamman ta UNESCO kan ingiza ilmantar da ’yan mata da mata, Peng ta yi kira ga al’ummar duniya da su hada hannu wajen karfafa koyar da sana’o’i da horar da mata, da karfafa karfin horar da mata a bangaren fasaha ta zamani, ta yadda za su ci gajiyar hakan, da samar musu makoma mai haske. Peng Liyuan ta kara da cewa, tana fatan hadin gwiwa da kowane bangare wajen ingiza samun kasaitaccen ci gaba kan aikin ilmantar da ’ya’ya mata, da ba da gudummawa wajen taimakawa mata wajen samun makoma mai haske. (Amina Xu)



















