Shugaban tawagar kasar Sin, wanda har ila yau shi ne shugaban sashin takaita yaduwar makamai na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Sun Xiaobo, wanda a yanzu haka yake halartar taron kwamitin kula da kwance damara da tsaron kasa da kasa na babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 81, ya gabatar da jawabi jiya Alhamis 8 ga watan nan, inda ya ce, gwamnatin Japan na gaggauta daukar matakan soja, wadda ta riga ta zama babban dalilin da ya haifar da barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki.
Sun Xiaobo ya ce, a lokacin da ta nemi izinin zama mambar MDD a shekarun baya, Japan ta amince cewa ta aikata munanan laifukan yaki, tare kuma da yarda da dukkanin abubuwan da ke akwai cikin kundin mulkin MDD. Amma gwamnatin Japan ta yanzu ta musanta tarihin kutsa kai cikin sauran kasashe, har ma ta yi yunkurin wanke kanta daga aikata munanan laifukan yaki, har ma ta nuna girmamawa ga wadanda suka aikata munanan laifukan yaki a lokacin yakin duniya na biyu.
Har wa yau, tana tsayawa ga inganta karfin soji da yayata makamai, da gaggauta daukar matakan soji, al’amarin da ya sa Japan ta zama wani babban dalilin da ya haifar da barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin.
Kudirin da Japan ta gabatar na kawar da “ka’idojin kasashe makiya” na kundin mulkin MDD, wani babban misali ne da ke shaida yunkurinta na kalubalantar tsarin tafiyar da huldar kasa da kasa da aka kafa bayan yakin duniya na biyu, tana mai fakewa da wani tsari da ta kira “maido da kwanciyar hankalin kasa”.
Sun Xiaobo ya kara da cewa, ya kamata Japan ta yi da-na-sanin laifukan da ta aikata na kutsa kai cikin sauran kasashen Asiya, da yin watsi da yunkurin sake daukar matakan soji kwata-kwata, tare kuma da daukar nauyin takaita yaduwar makaman nukiliya bisa dokokin kasa da kasa. (Murtala Zhang)














