Sin Na Aiwatar Da Matakan Shigewa Sahun Gaba A Fannonin Kimiyya Da Fasaha
A baya bayan nan ma’aikatar kimiyya da fasaha ta Sin ta sanar da aniyar gaggauta mayar da kasar Sin jagora, kuma mai samar da sabbin kirkire-kirkire, sabanin mai bayar da gudunmawa a fannonin kimiyya da fasaha, bayan da tuni Sin din ya zamo cikin muhimman kasashe dake da saurin samun karsashin ci gaban kirkire-kirkire. Alal hakika, wannan sako ne a bayyane wanda ke tabbatar da aniyar kasar ta zama mai cikakken ikon dogaro da kai, da karfin cin gajiyar fannonin kimiyya da fasaha, kuma kasa wadda ta rungumi wannan manufa cikin ginshikanta na wanzar da zamanantar da kai. Ana iya ganin kwazon kasar Sin a wannan fanni cikin tanadin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 da ake aiwatarwa tsakanin shekarar nan ta 2026 zuwa 2030, inda kasar ke kokarin amfani da ci gaban kimiyya da fasaha, wajen kyankyashe sabbin karfin samar da hajoji masu nagarta da ingiza kere-kere. Har ila yau, ana iya ganin yunkurin cimma wannan manufa, idan aka kalli adadin kasafin da kasar Sin ta shigar a fannin bincike da samar da ci gaba ko R&D, wanda darajarsa a shekarar 2025 da ta gabata ya haura kudin kasar yuan tirliyan 3.92, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 584.5, adadin da ya kai kaso 2.8 bisa dari na jimillar GDPn kasar. A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin ce kan gaba wajen yawan manyan dalibai masana kimiyya da fasaha, da fannin aikin injiniya, da lissafi, baya ga babbar kasuwar sayayya ta dijital dake ingiza kirkire-kirkire da kasar ke da ita. Kazalika, Sin na kan gaba wajen cin gajiyar fasahar intanet ta 5G, da fannin lissafin manyan na’urori masu kwakwalwa na quantum, da fasahar jirage marasa matuka. Masharhanta na ganin kasar Sin mai karin fasahohin kirkire-kirkire, za ta haifar da wani yanayi ga duniya baki daya, na cin gajiyar fasahohi daban daban. Wato dai ci gaban Sin a fannonin kimiyya da fasaha, zai bude karin kofofi da damarmaki ga dukkanin bil’adama, tare da a saita akalar duniya zuwa turbar bunkasar tattalin arziki mai game dukkanin sassa a gomman shekaru dake tafe.(Saminu Alhassan)



















