Masu Amfani Da Fasahar AI Mai Gudanar Da Ayyuka A Kasar Sin Sun Zarta Miliyan 700
Wani rahoto da aka fitar a Talatar nan, ya nuna cewa ya zuwa karshen watan Yunin bana, adadin masu amfani...
Wani rahoto da aka fitar a Talatar nan, ya nuna cewa ya zuwa karshen watan Yunin bana, adadin masu amfani...
Wasu rahotanni na cewa a ranar Juma’a 25 ga watan nan, hukumar lura da harkokin teku ta Philippines, ta fitar...
An gudanar da taron musamman game da batun yin kwaskwarima kan hanyoyin samun ci gaba na kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, a jiya Litinin 28 ga wannan wata, inda zaunanniyar wakiliyar Sin dake kungiyar WTO Li Yongjie ta yi nuni da cewa, a cikin shekaru fiye da 30 da aka kafa kungiyar WTO, yawan kasashe da yankuna na tattalin arziki masu tasowa da suka taka rawa a yayin bunkasa tattalin arziki da cinikayya na duniya ya karu, amma kasashe da yankuna masu tasowa sun fuskanci matsalolin kayyade fitar da kayayyaki iri-iri, da kuma raya karfin samar da kayayyaki da sauransu. Kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan maida fannin samun ci gaba a muhimmin matsayi, a yayin kwaskwarima ga kungiyar WTO, da kuma sa kaimi ga yin tattaunawa kan batun ta hanyar tambaya da bayar da amsa. Ya kamata daftarin da Sin ta gabatar a gun taron, ya taka muhimmiyar rawa wajen daidaita matsalolin da kungiyar ke fuskanta, amma ba tare da yin la’akari da kwamitoci da yarjejeniyoyi daban daban ba. Mahalartar taron sun nuna amincewa ga daftarin kasar Sin, kuma kasar Brazil, da kungiyar tarayyar Afirka, da kasashen Pakistan, da Indiya, da Indonesia da sauransu, sun nuna goyon baya ga mayar da samun ci gaba a matsayin tushen yin kwaskwarima, sun ce bai kamata a yi amfani da ma’auni guda wajen daidaita bukatun ci gaba daban daban ba.(Zainab Zhang)
Kasar Sin ta fitar da wani shiri na bunkasa masana’antar kera sabon samfurin batir a yayin gudanar da shirin bunkasa ci gaban kasa da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15 (2026-2030), inda ta kuduri aniyar cimma nasarar habaka masana’antar, da sabbin kirkire-kirkiren fasaha, da kuma ingancin kayayyaki. Shirin, wanda sassan gwamnati da dama suka fitar bisa hadin gwiwa ciki har da ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa, na da nufin tabbatar da ci gaban masana’antar mai dorewa da kuma kakkarfan kwazo wajen iya kirkire-kirkire a dukkan sassan tsarin masana’antar, nan da shekarar 2030. Kazalika, kasar Sin na da burin samun gagarumin ci gaba a fannin tsare-tsaren kera sabon batirin nan da shekarar 2030. Shirin ya yi tanadin fara yawaita amfani da dukkan baturan da aka kera a ma’auni mai girma, tare da tabbatar da cewa tsawon wa’adin aikin baturan lithium zai iya kunsar zagayen caji da amfani da su sau 15,000, nan da shekarar 2030. A cewar shirin dai, ana sa ran yawan baragurbin da ake samu a kayayyakin manyan kamfanoni zai ragu har ya kai matakin da ake auna shi da “kananan adadi cikin biliyan”, nan da shekarar 2030. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Fu Cong, zaunannen wakilin Sin dake MDD, ya fitar da jawabi a gun taron MDD da aka gudanar domin tunawa...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana cewa, babban aikin da ya rataya a wuyan Japan shi ne gyara katobara da kura-kuran shugabanninta kan batun Taiwan cikin gaggawa. Wang, wanda har ila yau shi ne darektan ofishin hukumar kula da harkokin waje na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta Sin (JKS) kuma mamba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da Takeshi Iwaya, shugaban kungiyar karfafa cinikayyar kasa da kasa ta Japan (JAPIT), a birnin Beijing. Wang ya bayyana cewa, babban abin da ke da muhimmanci shi ne rungumar nuna hali nagari dangane da batutuwan tarihi. Ya kara da cewa, ya kamata Japan ta samar da kyakkyawar fahimta da tunani mai kyau game da kasar Sin a matsayin ginshiki. Kazalika, Wang ya kuma ce ana fatan kungiyar JAPIT da dukkan mutane masu hangen nesa za su ci gaba da raya al’adar abota, da karfafa gwiwar Japan wajen daukar matakin da ya dace tare da bayar da amsa mai gamsarwa. A nasa bangare, Iwaya ya bayyana cewa, yanayin da dangantakar Japan da Sin ke ciki a yanzu abin damuwa ne. Inda ya ce bai kamata Japan ta manta da darussan da ta koya a baya ba, kuma ya zama wajibi ga ’yan siyasar Japan su jagoranci kasar a kan turbar da ta dace, tare da ci gaba da tsayawa tsayin daka kan tafarkin samun ci gaba cikin lumana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Kasar Sin ce ta mamaye teburin lambar yabo ta zinare a gasar nuna kwarewar aiki ta duniya karo na 48 da aka kammala jiya Lahadi da dare a birnin Shanghai, wannan ita ce gasa ta 5 a jere da kasar Sin ke lashe mafi yawan lambobin yabo. Chen Jining, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma sakataren kwamitin jam’iyyar na birnin Shanghai, da ‘dan majalisar gudanarwar kasar Sin Shen Yiqin, sun halarci bikin rufe gasar. ‘Yar kasar Sin He Xiaoman, ta samu lambar yabo mafi daraja ta alfarma ta Albert Vidal, saboda hazakar da ta nuna a gasar fasahar shimfida layin dogo. Wannan lambar karramawa ita ce mafi daraja da ake bayarwa ga ‘dan gasa mafi yawan maki a dukkan fannonin kwarewa. Kasar Sin ta fafata a fannonin kwarewa 64, inda ta lashe lambobin zinare 41 da azurfa 11, sai tagulla 4 da kuma lambobin yabo na kwarewa guda 6. Tawagar kasar Sin ce ta zo ta daya da yawan lambobin zinare, kuma ita ce ta samu lambobin yabo mafi yawa, da ma yawan makin rukunoni, don haka ta zama mafi hazaka a gasar ta nuna kwarewar aiki ta duniya. Kungiyar shirya gasar nuna kwarewa ta kasa da kasa ce ta shirya gasar da hadin gwiwar ma’aikatar kula da al’umma ta kasar Sin da gwamnatin birnin Shanghai. An gudanar da babban taro kan kwarewar aiki watau WorldSkills Conference na 2026 da kuma baje koli, yayin da ake gudanar da gasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Kasar Sin ta nuna mana karfinta da kwarewa a Gasar Nuna Kwarewar Aiki ta Duniya ta Shanghai ta 2026, watau WorldSkills Shanghai 2026, inda ta mamaye teburin lambobin yabo da ma yawan makin rukunoni, lamarin da ya ba tawagarta damar zama mafi hazaka a gasar. Yayin gasar ta kwanaki 5 da aka kammala jiya Lahadi, Sin ta lashe lambobin zinare 41 da azurfa 11 sai tagulla 4 da kuma lambobin yabo na kwarewa guda 6. Wannan ita ce gasa ta 5 a jere da ta samu mafi yawan lambobin yabo. Ni ganau ce na yadda aka shirya da gudanar da wannan gasa a birnin Shanghai. Kafin mu kai ga hazakar da tawagar kasar Sin ta nuna, kasar ta yi namijin kokari wajen shirya gudanar da wannan gasa. Domin an tsara komai bisa tsari da kwarewa, da yadda komai ya gudana cikin sauki ga masu baje kwarewarsu har da mu ’yan kallo. Wannan gasa dai, matasa ne masu jini a jika daga kasa da kasa suka mamaye ta tare da nuna basirarsu a bangarori daban-daban, kuma matasan kasar Sin ne suka yi zarra. Me nasarar da Sin ta samu ke nuna mana? A ganina hakan na da nasaba da kuduri mai karfi na gawamnatin kasar Sin, domin ta tsaya kai da fata wajen zuba jari da ci gaba da bayar da fifiko ga horo da koyar da sana’o’in hannu, wannan shi ya aza tubalin samar da kwararrun da gogewa da hazakarsu suka kai matakin kasa da kasa da kuma samun nasara. Ko kun san kasar Sin ta fafata a dukkan bangarori 64 na gasar? Wannan ya nuna cewa kasar Sin na hada shirye-shiryen bayar da horo da irin bukatun da ake da su, watau ta ko ina kasar na kokarin zama mai dogaro da kanta, ta hanyar amfani da albarkatun jama’a da take da su. Haka kuma, duk da cewa gasar ta shafi fasahohi na zamani da aiki da injuna, har yanzu akwai tsoffin sana’o’i da Sin ba ta yi watsi da su ba kamar aikin brikla (Bricklayer) da ta samu lambar zinare, lamarin da ke nuna cewa yayin da ake tafiya da zamani, har yanzu ana inganta tsoffin sana’o’i. Watau dai hazakar da tawagar kasar Sin ta nuna, daga cikinsu, ’yar kasar Sin He Xiaoman ta lashe lambar yabo mafi daraja ta gasar ta Albert Vidal Award, alama ce ta kishin kasa da kishin kai da irin kokari da gudunmawar da Sinawa maza da mata ke bayarwa wajen daukaka burin gwamnatin kasar na zama mai dogaro da kanta da kuma kyakkyawar jituwa da ke tsakanin gwamnati da al’ummar kasar. Hakika bai kamata a kalli nasarar Sin a matsayin nasara kadai don taya ta murna ba, akwai bukatar a dauke ta a matsayin darasi, domin ta nuna daraja da muhimmancin sana’o’in hannu. Yadda kasar ke bayar da muhimmanci ga sana’o’in hannu ya gina karfin al’umma na tsayawa da kafarsu da samar da aikin yi da wadata, wadanda su ne kashin bayan ci gaban al’umma da ci gaban kasa da uwa-uba zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma. (Fa’iza Mustapha)
A baya-bayan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin umarni, dangane da aiwatar da matakan samar...
Idan ana son ambatar sunayen kasashen da ke neman tabbatar da ci gaban kasashe daban daban na bai daya a duniya, to, ba za a rasa kasar Sin ba. Shugaban kasar, Xi Jinping, ya jaddada sau da dama cewa, “Ba zai yiwu a samu walwalar duniya da kwanciyar hankali bisa tushen mai kudi na kara samun kudi, yayin da mara kudi ke kara faduwa cikin kangin talauci ba.” Don daidaita yanayin rashin ci gaba dake damun dimbin kasashe, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar tabbatar da ci gaban duniya ta Global Development Initiative (GDI) shekaru 5 da suka gabata. Kana a kwanan baya, shugaban ya aika da sako ga taron manyan jami’ai kan cika shekaru 5 da gabatar da shawarar GDI da ya gudana a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka, inda ya sake nanata cewa, ci gaban tattalin arziki tushe ne na jin dadin rayuwar jama’a. Shawarar GDI ta kunshi bayanai masu nasaba da fannoni 6, wato dora matukar muhimmanci kan neman ci gaban tattalin arziki, da kokarin inganta rayuwar jama’a, da rage gibin dake tsakanin kasashe masu tasowa da masu sukuni, da amfani da fasahohin zamani don amfanar da al’ummun kasashe daban daban, da sauya salon tattalin arziki zuwa mai kare muhalli, da kokarin aiwatar da nagartattun manufofin da aka tsara. Cikin shekaru 5 da suka wuce, shawarar GDI ta samu karbuwa sosai a duniya. Zuwa yanzu, kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 130 sun goyi bayan shawarar, kana kasashe kusan 100 sun kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa tare da kasar Sin. Kana a bisa tsare-tsare masu alaka da shawarar, an ware kudin da yawansa ya kai fiye da dala biliyan 23, wajen gudanar da ayyukan hadin gwiwa masu amfanar da jama’a fiye da 1800, da horar da mutane masu neman koyon fasahohi fiye da dubu 200, da taimaka wa yunkurin raya tattalin arziki a kasashe fiye da 120. A kasar Najeriya ma ana iya ganin amfanin shawarar GDI. Wani bayanin da jaridar The Guardian ta kasar Najeriya ta watsa a kwanan baya ya ambata cewa, kasar Sin ta aiwatar da ayyuka da dama masu amfanawa jama’a a Najeriya, misali haka rijiyoyi, da kafa dakunan karatu da ake koyar da fasahohin dijital, da yayata fasahar noman shinkafar da aka tagwaita irinta, da samar da tallafin na’urorin da ake bukata a asibitoci, da dai sauransu. Kana a cikin ayyukan, aikin gina gandun noman laimar kwado ya janyo hankali sosai, har ma ma’aikatar aikin gona ta kasar Najeriya ta bayyana shi a matsayin nasarar da aka samu a fannin kokarin neman samun isasshen abinci. Kasar Sin ta nuna wa duniya ra’ayinta na tabbatar da ci gaban kasashe daban daban, ta hanyar gabatar da shawarar GDI shekaru 5 da suka wuce, wadda ta yi matukar kokarin aiwatarwa daga bisani. Hakan ya shaida cewa, kasar Sin aminiya ce ga duk wata kasa dake neman raya tattalin arzikinta. (Bello Wang)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.