Xi Jinping Da Manyan Jami’an JKS Da Na Kasa Sun Halarci Bikin Aza Furanni Na Karrama ’Yan Mazan Jiya Albarkacin Ranar Jaruman Kasa
A yau Laraba da safe, an kaddamar da bikin aza kwandunan furanni na karrama ’yan mazan jiya albarkacin ranar jaruman kasa a filin Tian’anmen dake birnin Beijing, inda manyan shugabannin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da na kasa, da suka hada da Xi Jinping da sauransu, da kuma wakilai daga bangarori daban daban, suka halarci bikin. Da karfe 10 na safiyar yau, aka fara bikin a hukumance. Shugaba Xi Jinping da manyan jami’an JKS da na kasa, sun hau kan dandamalin wurin tunawa da jaruman kasa, sa’an nan, suka tsaya a gaban kwandunan furannin. Daga bisani, Xi Jinping ya matsa gaba don gyara ribon din dake kan kwandunan furanni. Bayan haka, Xi Jinping da sauran shugabannin JKS da na kasa sun yi tafiya a hankali suna zagaya wurin tunawa da jaruman na kasa domin nuna girmamawa. Bana, shekara ce ta cika shekaru 105 da kafuwar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shekara ce ta cika shekaru 90 da cimma nasarar Doguwar Tafiya ta jar rundunar sojojin kasar Sin. Bisa jagorancin kwamitin tsakiyar JKS dake karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, dukkanin ’yan jam’iyyar da sojoji da kuma al’ummomin kabilu daban daban a kasar Sin, suna bin ruhin kafuwar JKS, da ruhin Doguwar Tafiya mai girma, inda suka nuna kwarin gwiwa da yin hadin gwiwa, domin gina kasa mai karfi da neman farfadowar kasa a dukkanin fannoni ta hanyar zamanantarwa. (Mai Fassara: Maryam Yang)



















