Al’ummar Sin Sama Da Biliyan 1.4, Kashin BayanCi Gaban Kasar
Kasar Sin ta fitar da wata takardar bayani a ranar Asabar, wadda ta ce a shekarun baya-bayan nan, tsarin ilimin sana’o’i na kasar, yana samar da matsakaicin adadi na kwararrun ma’aikata miliyan 10 ga masana’antu daban-daban a duk shekara. Mun saba da jin “in dambu ya yi yawa ba ya jin mai” a matsayin dalili ko kuma hanyar lullube gazawar wani tsari. Tabbas ina da yakinin mutane da dama kamar ni, sun amince da hakan. Sai dai, zamana a kasar Sin da abubuwan da na shaida, sun fahimtar da ni cewa, “duk yawan dambu zai ji mai, sai dai in ba a zuba isasshe ba.” Kuma “yawan dambu” ba matsala ba ce, maimakon haka, hanya ce ta samun arziki da dogaro da kai. “Dambu” a nan na nufin jama’a. A kasar Sin ne na ga yadda yawan jama’a ya zama alheri da hanyar samun wadata da dogaro da kai. Maimakon yawan jama’a ya zama tasgaro ga ci gaban kasar, sai ya zama karfin da ke ingiza ci gaba da wadata da kwanciyar hankalinta. Rashin aikin yi na zama babban dalilin dake haifar da talauci da aikata laifuffuka kamar sace-sace da fashi da makami, da tashe-tashen hankula da ake samu a cikin kasa. Sanin hakan ne ya sa kasar Sin tashi tsaye wajen bunkasa samar da ilimin fasahohi da sana’o’in hannu, domin samar da guraben aikin yi da kwararru, wanda zuwa yanzu ya kara karkata ga inganta kwarewa da biyan bukatun da masana’antun kasar ke da su. Kasar Sin na da kimanin makarantun koyar da sana’o’i sama da 10,000 da suka hada da na matakin sakandare da na gaba da sakandare, wadanda ke da dalibai sama da 30,000. Wannan mataki ya ba yara da matasa damar gano basirar da suke da ita, da bayar da gudunmawa ga cimma burikansu. Haka kuma, wata hanya ce ta ba dalibai samun kwarin gwiwa, domin za su samu bangarorin da suka fi sha’awa da basira a kai don raya su. Wannan ya saba da tsarin nan na lallai sai an yi karatu kan wasu takaitattun fannoni da watakila dalibi ba shi da sha’awarsu. Mutane sun bambanta, watau yayin da wani ke son karatun zube, wani kwarewarsa na ga bangaren abubuwan da zai iya yi da hannayensa. Wannan tsari na Sin yana ba da gudunmawa ga ci gaban kasa ta hanyoyi daban-daban, daga rage zaman kashe wando da aikata laifuka, zuwa biyan bukatun kasa da zama mai dogaro da kai da samar da al’umma mai ilimi da yaki da talauci da sauransu. Kuma shi ya ba kasar damar zama na daya a duniya a bangarori daban daban. Idan ba a manta ba, kasar Sin ce ta lashe gasar nuna kwarewar aiki ta kasa da kasa da aka yi a baya-bayan nan a birnin Shanghai a karo na 5 a jere, inda ta mamaye teburin lambobin yabo, ta lashe lambobin zinare 41 da azurfa 11 sai tagulla 4 da kuma lambobin yabo na kwarewa guda 6. Hakika duk kasar da ta jajirce wajen wadata al’ummarta da ilimi daidai gwargado, ta ba matasanta damar nakaltar sana’o’i, to ta yi nisa a tafarkin ci gaba mai inganci, kuma ba makawa, ta tabbatar da tsara kyakkyawar makomarta. (Faeza Mustapha)



















