Ka’idoji Hudu Da Shugaba Xi Ya Gabatar Na Da Matukar Muhimmanci A Fannin Tunkarar Manyan Matsalolin Afirka
Kwanan baya, yayin ganawarsa da shugaban majalisar ministocin kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wasu kaidoji 4, game da yadda bangarori daban-daban za su shiga a dama da su a fannin warware manyan batutuwan da ke ci wa nahiyar Afrika tuwo a kwarya. Dangane da wannan batu, mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana cewa, wadannan kaidoji suna da matukar muhimmanci wajen tunkarar manyan matsalolin da kasashen Afirka suke fuskanta, ciki har da halin da ake ciki a yanzu a yankin Kahon Afirka. Mao Ning ta kara da cewa, kaida ta farko ita ce, daukaka shugabancin Afrika, watau alummar nahiyar ne ya kamata su zama jigon jagorantar harkokinta. Kaida ta biyu, ita ce kiyaye adalci da gaskiya, watau ya kamata bangarori masu ruwa da tsaki su kiyaye manufofi da kaidojin kundin tsarin dokokin MDD, da girmama cikakken yanci da ikon kasashe masu ruwa da tsaki. Kaida ta uku, ita ce dakatar da rikice-rikice da wanzar da zaman lafiya. Kasancewar yaki da kakaba takunkumai daga bangare guda, ba za su warware rikice-rikice tsakanin kasa da kasa ba, don haka ya zama wajibi a nacewa martaba juna, da tuntubar juna, da neman yanayin da zai karbu ga kowa tare da hakuri da bambance-bambance, da fahimta da hakuri da juna. Sai kaida ta hudu, watau magance alamomi da tushen matsaloli. Ya ce ya kamata a yi kokarin mayar da hankali kan bukatun tsaro na gaggawa, yayin da ake tsara hanyoyin samun ci gaba mai dorewa. (Mai Fassara: Maryam Yang)



















