Hukumomin Lura Da Hada-hadar Kudi Na Sin Sun Sanar Da Sabbin Matakai Yayin Dandalin Shekarar Nan Ta 2026
Gwamnan babban bankin alummar kasar Sin Pan Gongsheng, ya ce za a kaddamar da matakin samar da tallafin tsabar kudade da nufin taimakawa cibiyoyin hada-hada da ba bankuna ba, ta yadda za su samu ikon biyan basussuka. Pan Gongsheng, ya bayyana hakan ne a Litinin din nan, yayin bikin kaddamar da dandalin tattauna batutuwan hada-hadar kudi na shekarar nan ta 2026 a birnin Beijing, dandalin da ya samar da zarfin musayar raayoyi tsakanin kusoshin manyan hukumomin dake lura da hada-hadar kudade na kasar Sin, dangane da manufofin da suke baiwa fifiko. Pan, ya kuma yi karin haske game da tanade-tanade masu fadi dake kunshe cikin matakan inganta hada-hadar kudade, ciki har da kyautata kaidin farashin basussuka, da kyautata tsarin gudanar da cinikayyar ketare tsakanin hukumomi masu ruwa da tsaki, ta amfani da kudin Sin wato yuan a kasuwar musayar kudade ta kasar. A daya bangaren kuma, shugaban babbar hukumar lura da hada-hadar kudade ta kasar Sin Ding Xiangqun, ya ce Sin za ta ci gaba da ingiza bude kofa a fannin hada-hadar kudade, da yiwa karin cibiyoyin hada-hadar kudi na ketare maraba, da kuma karbar karin kudaden jari na dogon zango. Dandalin tattauna batutuwan hada-hadar kudi na shekarar nan ta 2026, na gudana ne tun daga yau Litinin 19 zuwa 22 ga watan nan na Oktoba a birnin Beijing, ya kuma hallara manyan baki sama da 400 daga kasashe da yankunan duniya sama da 40. (Saminu Alhassan)



















