Sin Ta Fayyace Kamfanoni 500 Masu Zaman Kansu Mafi Karfin Jari A Shekarar 2026
A yau Talata ne Sin ta fitar da sunayen kamfanoni 500 masu zaman kansu a kasar, wadanda kuma suke kan...
A yau Talata ne Sin ta fitar da sunayen kamfanoni 500 masu zaman kansu a kasar, wadanda kuma suke kan...
Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta Sin(JKS), ya aika da sakon taya murna da gaisuwa ta musamman a madadin kwamitin tsakiya na JKS ga manoma da sauran masu aiki a sahun gaba a fannin noma da raya karkara, gabanin bikin girbi na manoman kasar Sin karo na tara. Xi, wanda har ila yau shi ne shugaban kasar Sin kuma shugaban hukumar soja ta tsakiya, ya jaddada muhimmancin daukar kwararan matakai don raya yankunan karkara a dukkan fannoni, tare da tabbatar da cewa manoma suna gudanar da kyakkyawar rayuwa cikin farin ciki. Xi ya yi nuni da cewa, a bana, yawan hatsin da aka girbe lokacin zafi a kasar Sin ya kai wani sabon matsayi, yayin da yawan shinkafar da ake girbewa da wuri ya ci gaba da dorewa ba tare da tangarda ba, kana ana sa ran samun girbi mai albarka a lokacin kaka. Kazalika, ya ce ya kamata kwamitocin jam’iyya da hukumomin gwamnati a dukkan matakai su yi aiki don tabbatar da cewa manufofin da aka samar da nufin karfafa aikin gona, da amfanar da manoma, da kuma habaka yankunan karkara sun haifar da gagarumin sakamako mai kyau, tare da kara karfin noma amfanin gona baki daya, da habaka inganci da kwazon sashen aikin gona. Bikin girbi na manoman kasar Sin dai biki ne na matakin kasa na farko da aka kirkiro musamman domin manoman kasar. A bana, bikin zai gudana ne a gobe Laraba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Bisa gayyatar shugaban Amurka Trump, shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai je ziyarar aiki a Amurka daga ranar 23 zuwa 25 ga watan Satumba. Wannan na nuna komawar shugaba Xi Amurka bayan shekaru uku, kuma za ta zamo cikon ziyarar juna tsakanin shugabannin Sin da Amurka cikin rabin shekara. Ziyarar tana nuna wata alama mai kyau ga duniya cewa bangarorin biyu suna ci gaba da zurfafa dangantaka “mai ma’ana bisa manyan tsare-tsare cikin kwanciyar hankali”. Wani bincike na jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a tsakanin mutane 12,000 a sassan kasashe 39 na duniya ya nuna cewa kashi 75% na wadanda suka bayyana ra’ayoyin, sun yi amannar cewa dangantaka mai dorewa cikin kwanciyar hankali a tsakanin Sin da Amurka tana da matukar muhimmanci ga al’ummar duniya. Adadin mutanen ya karu zuwa kashi 78.3% a kasashe masu tasowa, yayin da kashi 76.7% na wadanda suka bayyana ra’ayoyi daga Amurka kuma suka kasance masu irin wannan ra’ayi. Dangantaka mai dorewa cikin kwanciyar hankali tsakanin Sin da Amurka na taimakawa wajen kara tabbatar da zaman lafiya a duniya. Wannan ganawa tsakanin shugabannin kasashen biyu tana da muhimmanci ga kyautata jin dadin al’ummomin biyu, da kuma samun ci gaba da wadata a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta goyi bayan bukatar ma’aikatan gwamnati na ganin an ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N500,000,...
Rundunar Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) ta kai samame wata masana’anta da ake zargin tana haɗa gurɓataccen ruwan ’ya’yan...
Mataimakin firaministan gwamnatin kasar Sin He Lifeng, da sakataren kudi na Amurka Scott Bessent, da wakilin kasuwanci na kasar Jamieson...
Ma’aikatar raya masana’antu da fasahohin sadarwa ta kasar Sin, ta ce gwamnatin kasar ta sha alwashin zakulowa, da tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu da ake da kyakkyawan fatan bunkasarsu. Ma’aikatar ta ce maimakon jiran har sai irin wadannan masana’antu sun nuna bukatarsu ta neman taimako, gwamnati za ta himmatu wajen lalubo su da tallafa musu yadda ya kamata. Karkashin hakan, ma’aikatar za ta kyautata tsarin tallafinta ga irin wadannan masana’antu, musamman masu amfani da fasahohin zamani da kwarewa, ta yadda za su kai ga sarrafa hajoji masu kima da fice tsakanin nau’o’insu, kana za a matsa kaimi wajen lalubo sabbin kamfanoni da ake ganin za su ciri tuta a nan gaba, musamman ma wadanda ke mayar da hankali ga ayyuka masu kunshe da fasahohin kirkire-kirkire, da masu bunkasa sabbin hajoji. A jiya Lahadi ne ma’aikatar ta alkawarta hakan, yayin wani taron masu ruwa da tsaki, yayin tattaunawa dangane da hanyoyin kyautata tsarin bincikowa, da samar da karin hidimomi ga irin wadannan masana’antu. Wani jami’in ma’aikatar ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da inganta tsarin shari’a da manufofin gudanarwa, da shirye-shiryen kyakkyashe masana’antu, da tallafawa ’yan kasuwa da hidimomi ta yadda za a kai ga ingiza ci gaba mai nagarta tsakanin kanana da matsakaitan masana’antu. Kazalika, za a ci gaba da karfafa gwiwar kamfanoni ta yadda za su kai ga cimma muradun kwarewa, da ci gaban kirkire-kirkire, da fadada bincike da samar da ci gaban harkokin zuba jari, da kokarin cimma sabbin nasarori a muhimman fasahohi. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta Sin, Guo Jiakun, ya bayyana a yau Litinin cewa, a ranar 25...
’Yan bindiga sun kai hari garin Dukura, da ke ƙaramar hukumar Kebbe a Jihar Sokoto, inda suka kashe mutane biyu...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da ƙarin kashi 95 cikin 100 na albashin ma’aikatan lafiya a faɗin jihar, inda sabon...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.