Yau 9 ga watan Satumba, babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta Sin, kana shugaban kasar Xi Jinping, ya aika da sakon taya murna ga babban sakataren jam’iyyar ‘yan kwadago ta Koriya ta Arewa, kana shugaban majalisar gudanarwa ta Koriya ta Arewa Kim Jong-un, dangane da bikin cika shekaru 78 da kafuwar jamhuriyar dimokuradiyya ta al’ummar Koriya ta Arewa.
A cikin sakonsa Xi ya nuna cewa, a cikin shekaru 78 da suka gabata, al’ummar Koriya ta Arewa sun dogara da kansu, da hada kai wajen yin gwagwarmaya, da kuma ciyar da ayyukan gurguzu na Koriya ta Arewa gaba a fannoni daban-daban bisa jagorancin jam’iyyar ta kwadago.
Musamman a ‘yan shekarun nan, babban jagora Kim Jong-un ya jagoranci jam’iyyar da al’ummar Koriya ta Arewa, inda suka himmatu wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma, tare da samun jerin nasarori, kuma bangaren Sin yana farin ciki da hakan.
Xi ya kara da cewa, a watan Yuni na bana, ya kai ziyarar aiki a kasar, inda shugabannin biyu suka sake ganawa da juna, matakin da ya bude sabon babi na ci gaban dangantakar jam’iyyu da kasashen biyu.
Yana mai fatan kara hadin gwiwarsu don ci gaba da karfafa ba da jagoranci ga dangantakar jam’iyyu da kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, da zurfafa ayyukan jam’iyyu da kasashen biyu, da kuma ciyar da jin dadin al’ummomin kasashen biyu da abota gaba, dadin dadawa kuma da bayar da gagarumar gudunmawa don inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba da samun wadata mai dorewa a yankin da ma duniya baki daya. (Amina Xu)














