Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana
Alkaluman da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta samar sun shaida cewa, daga watan Janairu zuwa Agusta na wannan shekara,...
Alkaluman da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta samar sun shaida cewa, daga watan Janairu zuwa Agusta na wannan shekara,...
Bisa kididdigar da hukumar aike da sakwanni ta kasar Sin ta bayar, an ce, sana’ar aike da sakwanni a Sin, ta ci gaba da bunkasa cikin kwanciyar hankali daga watan Janairu zuwa watan Agustan bana. Masana’antar na mai da hankali kan bukatun kasuwa na jigilar kayan gwari da kayayyakin gona da abincin teku na musamman, kuma tana ci gaba da inganta ayyukan jigilar kayayyaki. Sabbin alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa watan Agustan bana, jimillar ayyukan jigilar kayayyaki ta kai biliyan 145.46, wadda ta karu da kashi 4.0% idan an kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma kudaden shiga a wannan bangare (ba tare da kudaden shiga dake shafar kudin ajiya a bankin tura sakonni na Postal Savings ba) ya kai Yuan triliyan 1.23045, wanda ya karu da kashi 6.0% idan an kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma sana’ar gaba daya na ci gaba da habaka cikin kwanciyar hankali. (Amina Xu) Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar HankaliBisa kididdigar da hukumar aike...
A yau Juma’a 18 ga wata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya jagoranci taron manema labarai da...
Kwamitin kare hakkin dan adam na MDD na gudanar da taro na 63 a Geneva. Kwanan nan, wakilin Sin ya yi kira a yayin taron da a kara mai da hankali a fannin tattalin arziki, zamantakewa da al’adu. Wannan kira ya shafi ainihin bukatun kasashen Afirka, abin da al’ummar Afirka ke mai da hankali a gaban kome shi ne, ko za a iya fita daga talauci, ko za a iya samun ci gaba, ko za a iya wadata, har ma ko za a iya rayuwa? A ganinsu, hakkin dan adam ba wata alama ta siyasa ba ce kawai. Kwamitin kare hakkin dan adam yana da tsare-tsare guda 13 na musamman mai bincike kan kasa da kasa, dukkansu suna mai da muhimmanci kan kasashe masu tasowa, suna kashe miliyoyin daloli, amma ba su mayar da hankali sosai kan matsalolin hakkin dan adam da suke fi bukatar kulawa ba. Yayin da ’yan siyasar kasashen yamma ke yada jita-jita da labaran karya da nuna fuska ta biyu, a wani bangare kuwa yankin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kango na fuskantar bala’in jin kai sakamakon rikicin makamai, kuma sama da mutane miliyan 30 a Sudan na bukatar taimakon jin kai. Wasu kasashe suna sha’awar mayar da kwamitin kare hakkin dan adam fagen takara a bangare siyasa, yayin da kasashe masu tasowa da dama, musamman kasashen Afirka, ke fuskantar karancin ci gaba da matsalolin rayuwar al’umma, amma ana barin su a gefe. A daya bangaren kuma, ayyukan Sin wajen tabbatar da hakkin tattalin arziki, zamantakewa da al’adu na da amfani mai ma’ana ga Afirka. Sin ta kammala aikin kawar da talauci a kan lokaci, mutane miliyan 98.99 na karkara dake cikin talauci duk sun fito daga kangin talauci, kuma gundumomi 832 masu fama da talauci ma dukkansu sun kawar da kangin talauci. Sama da mutane biliyan 1.3 a Sin suna cikin tsarin inshorar lafiya mai tushe, kuma adadin masu shiga ya tsaya tsayin daka sama da kashi 95%. Nasarorin da Sin ke samu wajen kare hakkin dan adam marawa Sin bayan wajen shiga harkokin kula da hakkin dan adam na duniya, kuma irin wannan dabara abin da Afirka ta fi bukata ke nan. Hadin gwiwar Sin da Afirka na ci gaba da bin ka’idar “Guntun gatarinka ya fi sari ka ba ni” don taimakawa Afirka ta kara bunkasa ci gaban kanta, kuma wannan shi ne mataki mafi amfani wajen tabbatar da hakkin tattalin arziki, zamantakewa da al’adu. A fannin tabbatar da isashen abinci, Sin na yada fasahar shinkafa mai sauri a kasashen Zimbabwe da Chadi. A lardin Mashonaland ta Yamma na Zimbabwe, kwararrun Sin sun kafa “gidan renon kaji”. A kauyen Medken na Chadi, gonar misali ta samar da shinkafa ton 10.03 a kowace hekta, wanda ya kai kusan ninki 3 na matsakaicin yawan amfanin gona na yankin. A fannin kiwo lafiya kuwa, cikin fiye da shekaru 60 da suka gabata, tawagar likitocin Sin dake taimakawa Afirka sun tura kusan ma’aikata 26,000 zuwa kasashen Afirka 48, suna jinyar marasa lafiya miliyan 230. A shekarar 2026, lokacin da annobar Ebola ta barke a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kango, Sin ta tura tawagogin kwararrun likitocin yaki da annobar sau 3 a jere. A yayin taro na 63 na kwamitin kare hakkin dan adam, wakilin Sin ya yi kira da a kara mai da hankali a fannin tattalin arziki, zamantakewa da al’adu. Wannan shi ne abin da Sin ke yi a cikin gida da kuma a nahiyar Afirka. Yayin da wasu kasashe ke daukar hakkin dan adam a matsayin makamin siyasa na tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu kasashe, Sin tana kokarin tura kayan aikin noma na zamani, iri da magunguna da fasaha zuwa kasashen Afirka, don taimaka musu wajen kawar da talauci da samun ci gaba da wadata. Wane ya dauki ainihin matakan tabbatar da hakkin dan adam? Al’ummar Afirka za su iya ganewa idanunsu da kansu. (Marubuciya: MINA)
Shugaban hukumar ba da taimakon fasaha da kwararru ta Najeriya NTAC General Yusuf Buba Yakub, ya bayyana cewa, Najeriya na daukar darasi daga kyakkwar alakar diflomasiyya da jan hankali da kasar Sin ke amfani da shi, a kokarin da kasar ke yi na karfafa tasirinta a duniya, da karfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, ta hanyar aikewa da taimakon kwararun ma’aikata zuwa kasashe. Yakubu ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin kasar, inda ya ba da misali da salon da Sin ke amfani da shi na hulda da kasashen waje, domin gina doguwar alaka ta hanyar hadin gwiwa. Tun bayan kirkirar hukumar NTAC a shekarar 1987, ta tura ’yan Najeriya kwararru ’yan sa-kai sama da 10,000 zuwa kasashe sama da 40 a daukacin nahiyar Africa da yankin Caribbean da tsibiran Pacific, inda kwararrun suka bayar da gudummawa a fannoni da dama, da suka hada da fannin ilmi, magunguna, shari’a, injiniya, noma da kuma fasaha. (Mai Fassara: Suleiman Suleiman)
Ministan kula da harkokin wajen Burundi Edouard Bizimana, ya ce tafarkin Sin na samun ci gaba bisa dogaro da karfinta,...
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi hira da sakataren harkokin waje na Amurka Marco Rubio ta wayar tarho a jiya 17 ga watan Satumba. Bangarorin biyu sun tattauna sosai kan cudanya tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu. Wang Yi ya ce, dangantakar Sin da Amurka na tafiya yadda ya kamata bisa manyan tsare-tsare da shugabannin kasashen biyu suka tsara a baya-baya nan, matakin da ya dace da bukatu da fatan al'ummar duniya. Wang Yi, ya jaddada cewa, tuntubar shugabannin kasashensu muhimmin karfi ne na tabbatar da huldar Sin da Amurka, kuma ya kamata bangarorin biyu su share fagen mu'ammalar shugabannin kasashen a karo mai zuwa bisa tushen daidaito, girmama juna da cin moriya tare, kana da karfafa mu'ammala da ingiza hadin gwiwa da daidaita bambancin ra'ayi da mutunta muradunsu, ta yadda za a samar da sako mai kyau na kokarin ingiza huldar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, da karfafa zaman lafiya da ci gaban duniya. Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun kuma yi musayar ra'ayi kan halin da ake ciki a yankin Gabas Ta Tsakiya da sauransu.(Amina Xu) Wang Yi Ya Yi Hira Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio Ta Wayar TarhoMinistan harkokin...
Yau 17 ga wata, Sin ta fitar da "Rahoton Ci Gaban Cinikin Shige Da Fice Mai Dorewa Ba Tare Da...
A yau Alhamis ne aka gudanar da dandalin tattauna batutuwan zaman lafiya da tsaro na Sin da nahiyar Afirka karo na hudu a nan birnin Beijing. Taron ya gudana ne karkashin jigon "Gina tsaro tare: Shekaru 70 na goyon bayan juna, yin aiki kafada-da-kafada a sabon zamani", ya kuma hallara wakilai daga sassan hukumomin tsaro, da na soji, da jakadun da ke aiki a nan kasar Sin na kasashe membobin kungiyar Tarayyar Afirka ta AU da kasashen Afirka 41. Ministan ma’aikatar tsaron kasar Sin Dong Jun, ya halarci taron tare da gabatar da jawabi. A cikin jawabin nasa Dong Jun, ya ce a bana ake bikin cika shekaru 70 da kafa huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kasashen Afirka. Kuma hadin gwiwar tsaro tsakanin Sin da nahiyar Afirka ya haifar da ci gaban sassan biyu, da ma daidaiton yanayin kasa da kasa. Kazalika, ya ce kamata ya yi sassan biyu su aiwatar da matakan wanzar da kawancen gargajiya, da dagewa wajen bin turbar hadin gwiwa ta tsawon lokaci, wanda ke wakana bisa zaman daidai-wa-daida da cimma moriya tare. Ministan tsaron na Sin ya kara da cewa, rundunar sojojin kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da bangaren kasashen Afirka wajen karfafa tsare-tsare, da inganta tsarin musayar tsaro mai game dukkanin fannoni, kuma mai matakai daban daban, da zurfafa hadin gwiwar tsaron teku na shiyyoyi, da kyautata ikon wanzar da tsaro a sabbin fannoni, da samar da karin nasarori na hakika, ta yadda za a iya bayar da sabbin gudunmawa wajen gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a sabon zamani daga dukkanin fannoni. A nasu bangaren, wakilan Afirka a taron sun jinjinawa rawar da kasar Sin ke takawa, a matsayinta na muhimmiyar kawa ga kasashen Afirka, suna masu bayyana yadda tsaron nahiyar ya hade cikin na sauran sassan duniya. Har ila yau, sun kuma bayyana aniyarsu ta kara karfafa hadin gwiwa da Sin a harkokin tsaro, kana da bayar da gudunmawa ga ci gaban alakar Afirka da Sin. (Saminu Alhassan)
Ga duk mai bibiyar irin ci gaban da kungiyar BRICS ke samu a shekarun baya bayan nan, ya kwana da...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.