ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Zamu Laminci Maguɗin Zaɓe Ba – Atiku

by Abubakar Sulaiman
2 weeks ago

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fito fili ta bayyana dalilan sauye-sauyen da aka ruwaito an yi wa wasu manyan jami’anta, da kuma kamfanonin da za su buga muhimman kayan zaɓen shekarar 2027.

Atiku ya ce dole ne hukumar ta tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa tsarin gudanar da zaɓen yana tafiya bisa gaskiya, adalci da bin doka.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaransa, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Asabar, Atiku ya ce rahotannin sauya wasu jami’ai a sashin gudanar da zaɓe na INEC na buƙatar bayanin gaggawar.

ADVERTISEMENT

Rahotannin sun nuna cewa an mayar da Darakta Isa Magaji Gum daga sashin gudanar da zaɓe zuwa sashin rajistar masu zaɓe, yayin da aka naɗa Oluyemi Titilayo Adeyemi-Showunmi domin jagorantar sashin gudanar da zaɓe. An kuma bayyana Dr Lawrence Bayode a matsayin shugaban sashin fasahar sadarwa da kwamfuta (ICT).

Atiku ya ce sassan gudanar da zaɓe, da rajistar masu zaɓe da fasahar sadarwa suna da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da zaɓe, don haka ya kamata INEC ta bayyana ƙa’idojin da ta bi wajen naɗe-naɗe da sauya ma’aikata.

LABARAI MASU NASABA

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

ADC Ta Yi Wa APC Ba’a Kan Zargin Hayar Taron Jama’a Da Rashin Cika Kujeru A Taron Kaduna

Ya kuma jaddada cewa bai kamata a ɗauki wani jami’i a matsayin wanda ba zai iya yin aikinsa yadda ya kamata ba saboda ƙabila ko asalinsa ba, amma duk wani rahoto da zai iya haifar da shakku kan siyasa na buƙatar sahihin bayani daga hukumar.

Haka kuma, Atiku ya buƙaci INEC ta tabbatar ko ta musanta rahotannin da ke cewa kamfanin Hitech ko wani kamfani mai alaƙa da shi ya samu kwangilar buga muhimman kayan zaɓen 2027. Ya ce bayanan da suka same shi sun nuna yiwuwar ware sama da rabin kayan zaɓen, ciki har da kayan zaɓen shugaban ƙasa, ga wani kamfani da ba a bayyana sunansa ba, wanda ake zargin yana Faransa.

Ya kuma ambaci rahotannin cewa kamfanin Nigerian Security Printing and Minting Plc (NSPMC) zai buga kayan zaɓe na jihohi 15 zuwa 17 kawai, yayin da kamfanoni masu zaman kansu za su kula da sauran jihohin. Atiku ya buƙaci a bayyana sunayen kamfanonin, kuɗin kwangiloli, hanyoyin bayar da su da matakan tsaro da za a bi wajen samarwa, adanawa da jigilar kayan zaɓen.

Ya kuma yi gargaɗin cewa bai kamata a bai wa Hitech ko wani kamfani mai alaƙa da shi kwangilar buga kayan zaɓe masu muhimmanci ba, yana mai danganta damuwarsa da rahotannin alaƙar kasuwanci tsakanin iyalan Chagoury, masu kamfanin Hitech, da iyalan Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Atiku ya kuma buƙaci a binciki yadda aka bayar da manyan kwangilolin gwamnati ga Hitech, ciki har da aikin Babbar Hanyar Teku ta Legas zuwa Kalaba (Lagos-Calabar Coastal Highway).

Atiku ya yi kira ga INEC da ta yi amfani da ƙarfin masana’antun buga takardu masu tsaro na cikin gida, tare da tabbatar da cewa ana iya bin diddigin yadda ake sarrafa takardun zaɓe daga lokacin buga su har zuwa isar da su. Ya kuma buƙaci Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana rabon kwangilolin buga manyan takardun kuɗi da matsayin kamfanin NSPMC da ’yan kwangilar ƙasashen waje.

Ya ce jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) za ta sa ido kan tsarin, tare da sanar da masu sa ido na cikin gida da na ƙasashen waje duk wani rashin gaskiya, yana mai cewa ’yan Nijeriya ba za su amince da sace musu ƙuri’u ba, kuma za su yi amfani da hanyoyin doka da dimokuraɗiyya wajen kare zaɓensu.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
  • Abubakar Sulaiman
    Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC
  • Abubakar Sulaiman
    Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

MASU ALAKA

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?
Siyasa

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

October 25, 2026
Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo
Siyasa

ADC Ta Yi Wa APC Ba’a Kan Zargin Hayar Taron Jama’a Da Rashin Cika Kujeru A Taron Kaduna

October 25, 2026
An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna
Manyan Labarai

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Next Post
Sin Ta Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Sauyin Yanayi Da Hadin Gwiwa A Babban Taron Arctic

Sin Ta Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Sauyin Yanayi Da Hadin Gwiwa A Babban Taron Arctic

LABARAI MASU NASABA

Malaman Makarantun Gwamnati A Abuja Za Su Tsunduma Yajin Aiki Daga Ranar Litinin

Peter Obi, Marowaci Ne Ba Zai Iya Shugabancin Nijeriya Ba – Wike

October 25, 2026
Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

October 25, 2026
Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Uku Da Aka Sace A Kebbi

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Uku Da Aka Sace A Kebbi

October 25, 2026
Ana Buƙatar Ɗaukar Matakai Masu Tsauri Domin Ci Gaban Nijeriya – Wike

Ana Buƙatar Ɗaukar Matakai Masu Tsauri Domin Ci Gaban Nijeriya – Wike

October 25, 2026
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Tura Dakarunta Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Yankin Olle-Bunu Na Jihar Kogi

Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 15 Ta Harin Sama A Borno

October 25, 2026
2027: Hana Tinubu Wa’adi Na Biyu Na Iya Jefa Nijeriya Cikin Rikicin Siyasa — Pakistan

Tinubu Ya Cancanci A Sake Zaɓensa A 2027 — Pakistan

October 25, 2026
Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Harin Jihar Taraba Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 40

Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Harin Jihar Taraba Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 40

October 25, 2026
Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo

ADC Ta Yi Wa APC Ba’a Kan Zargin Hayar Taron Jama’a Da Rashin Cika Kujeru A Taron Kaduna

October 25, 2026
An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.