ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Ayyukan Titunan Gwamnan Kaduna Suka Farfaɗo Da Ilimi Da Kiwon Lafiya Da Noma A Sabon Gari

by Shehu Yahaya
2 months ago
Kaduna

Ayyukan ginawa da inganta hanyoyi da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ke aiwatarwa sun fara haifar da sauyi mai ɗorewa a rayuwar al’ummar Ƙaramar Hukumar Sabon Gari da Zariya. 

Hanyar Dogon Bauchi zuwa Kakeyi, wacce ke da tsawon kilomita 17 tare da sabuwar gadar Kakeyi, ta zama wata babbar hanyar ci gaba da ta sauƙaƙa zirga-zirga, ta ƙara yawan yara masu shiga makaranta, ta rage asarar amfanin gona bayan girbi, tare da bunƙasa kasuwanci da tattalin arzikin yankin.

Hanyar ta taso ne daga bakin Masallacin Juma’a da ke Dogon Bauchi a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari zuwa Kakeyi da ke Ƙaramar Hukumar Zariya.  Hanyar za ta amfani al’ummomi sama da dubu ɗari biyar, musamman manoma, ƴan kasuwa da ɗalibai da suka shafe shekaru suna fama da matsalar rashin ingantacciyar hanya.

ADVERTISEMENT

Wannan ya fito fili ne yayin wata ziyarar tantance ayyukan raya ƙasa da tawagar ƴan jarida ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ta kai domin duba ayyukan da gwamnatin jihar ke aiwatarwa a sassa daban-daban.

A zantawar manema labarai, Mazauna yankunan Dogon Bauchi da Kakeyi sun bayyana cewa gina gadar Kakeyi da shimfiɗa kwalta ya kawo ƙarshen wahalhalun da suka jima suna fuskanta, musamman wajen zirga-zirga tsakanin ƙananan hukumomin Sabon Gari, Zariya da Soba.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

mazaunin garin Jaba, Shamsudeen Abdullahi ya ce sama da shekaru 30 manoma suna asarar amfanin gonarsu saboda rashin hanya mai kyau.

“Wannan gada da titin za su rage asarar kayan gona, su ƙara yawan masu zuwa kasuwanni, kuma sun haɗa dubban al’umma da suka dogara da noma da kasuwanci domin gudanar da rayuwarsu,” in ji shi.

Shi ma wani manomi, Ibrahim Abubakar, ya bayyana yadda rayuwarsu ta sauya bayan kammala aikin.

“Yanzu haka daga gona nake dawowa cikin motata. A da sai mun hau kwalekwale kafin mu isa gida. Allah kaɗai ya san adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon ambaliya da rashin gada.”

A ɓangaren ilimi kuwa, ɗaliban yankin sun ce sabon titin ya kawo ƙarshen wahalar da suke sha wajen zuwa makaranta. Sun bayyana cewa a baya dole ne su riƙa amfani da kwalekwale domin tsallakawa tsakanin Kakeyi da Dogon Bauchi, lamarin da ke janyo jinkiri da haɗarin rayuwa. Amma yanzu suna iya tafiya a ƙafa cikin ƴan mintuna kaɗan su isa makaranta cikin kwanciyar hankali.

Mazauna yankunan sun ce wannan sauyi ya ƙara yawan yaran da ke halartar makaranta, tare da rage yawan waɗanda ke daina karatu saboda matsalolin sufuri.

Sun gode wa Gwamna Uba Sani bisa aiwatar da ayyukan ci gaba da ya kawo musu wanda suka daɗe suna nema. Sun yi alƙawarin cewa suna jiran ranar da za su saka masa da biki. 

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce gwamnatin Sanata Uba Sani ta himmatu wajen samar da ingantattun hanyoyi domin bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar jama’a.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta gina hanyoyi sama da 150 a faɗin Kaduna, yana mai cewa titin Dogon Bauchi zuwa Kakeyi na daga cikin ayyukan da za su rage mace-macen mata masu juna biyu da marasa lafiya da ke faruwa sakamakon rashin hanyar zuwa cibiyoyin lafiya.

A cewarsa, aikin ba wai hanya kaɗai aka gina ba, an samar da wata gada ta ci gaba wacce za ta haɗa al’umma, ta bunƙasa ilimi, noma, kasuwanci da harkokin lafiya, tare da tabbatar da cewa al’ummomin karkara sun more romon dimokuraɗiyya kamar sauran sassan jihar.

Kaduna
Shehu Yahaya
+ postsBio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Gwamnan Katsina Ya Kai Ziyarar Duba Aikin Cibiyar Gyaran Motoci Mai Amfani Da Hasken Rana

Gwamnan Katsina Ya Kai Ziyarar Duba Aikin Cibiyar Gyaran Motoci Mai Amfani Da Hasken Rana

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.