ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bambancin Sin Da Amurka Bai Tsaya Kan Manufofi Kadai Ba

by Sulaiman
5 months ago
Amurka

Jaridar “The Hill” ta kasar Amurka, ta wallafa wani bayani a kwanan nan, mai taken “Kasar Sin ta samar da tabbaci ga kasashen Afirka, yayin da kasar Amurka ta kayyade musu wa’adi kadai”. Inda marubucin bayanin ya kwatanta manufofin ciniki na kasashen Amurka da Sin, yana mai cewa, kasar Amurka ta bar dokarta da ta shafi yafe wa wasu kasashen dake nahiyar Afirka harajin kwastam ta AGOA, ta zama mai zarce wa’adi, sa’an nan ko da yake ta tsawaita wa’adin dokar da shekara daya, amma ta sanya kasashen Afirka biyan karin harajin kwastam na kaso 15. Yayin da a nata bangare, kasar Sin ta yi alkawarin yafe wa dukkan kasashe 53 dake nahiyar Afirka da suka kulla huldar diflomasiyya da ita harajin kwastam.

Ganin haka ya sa marubucin ya shawarci kasar Amurka da ta daidaita manufar ciniki a kokarin “takara da kasar Sin”, domin a ganinsa muddin kasar Amurka ta gyara wasu manufofinta, to, za ta zama mai samun karbuwa kamar yadda kasar Sin take a Afirka. Sai dai a hakika, bambancin kasashen Sin da Amurka bai tsaya ne kan wasu manufofi kadai ba, har ma ya shafi wasu manyan akidu nasu.

Wani shehun malami dake aiki a jami’ar Harvard ta kasar Amurka, mai suna Stephen Walt, ya ce babbar akidar kasar Amurka ita ce zama mai kwatar dukiyoyi da albarkatu, da aiwatar da mulkin danniya a duniya. Wannan ra’ayi ya sa kasar son daukar matakan kashin kai, da nuna son kai da girman kai, da kokarin cin zarafin sauran kasashe. Zuwa yanzu, kasar Amurka ta janye jikinta daga kungiyoyin kasa da kasa 66, da karbar karin harajin kwastam kan kayayyakin sauran kasashe yadda ta ga dama. Sa’an nan, a kwanan baya, kasar Amurka ta far wa kasar Venezuela, da matsawa kasar Cuba lamba, tare da haifar da tashin hankali a yankin Latin Amurka, kafin daga bisani ta hada kai da kasar Isra’ila wajen kai hare-hare kan kasar Iran, inda ta haddasa bala’in jin kai, da haifar da matsala ga zirga-zirgar jiragen ruwa ta shigar teku ta Hormuz, da kuma girgizar farashin mai a kasuwannin duniya.

ADVERTISEMENT

A nata bangare, akidar da kasar Sin ta dauka akasin ta kasar Amurka ce. Yayin da duniyarmu ke fuskantar wani yanayi na tangal-tangal, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan yunkurin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki. A shekarun nan, kasar Sin ta gabatar da dimbin shawarwari masu muhimmanci, da suka shafi samar da ci gaban tattalin arziki, da tsaro a duniya, da kare al’adun gargajiya, da kula da al’amuran kasa da kasa yadda ya kamata. Kana a kokarin tinkarar tashin hankalin da ake fuskantar yanzu a yankin Gabas ta Tsakiya, kasar Sin ta shiga aikin sulhunta bangarori masu ruwa da tsaki, da neman daidaita lamarin karkashin tsarin Majalisar Dinkin Duniya, har ma ta hada hannu da kasar Pakistan wajen gabatar da wasu shawarwarin tabbatar da zaman lafiya, a kokarin daidaita rikicin da ake fuskantar.

Wannan bambancin ra’ayin dake tsakanin kasashen Sin da Amurka ya haifar da sakamako: kamar yadda wani sakamakon bincike da kamfanin Gallup mai gudanar da binciken ra’ayin jama’a na kasar Amurka ya gabatar a kwanan baya ya nuna, cewa yawan mutanen kasashe daban daban da suka yarda da kwarewar kasar Sin a fannin jagoranci a duniya ya kai kaso 36 a shekarar 2025, yayin da jimillar da kasar Amurka ta samu ita ce kaso 31. Inda wannan bambanci na kaso 5 ya zama mafi girma cikin dukkan sakamakon binciken da kamfanin Gallup ya gudanar cikin shekaru 20 da suka gabata.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Dalilin da ya sa ake samun bambanci wajen amincewa tsakanin kasashen Sin da Amurka, shi ne kasashen biyu na rungumar akidu daban daban, inda akidar Amurka ita ce mulkin danniya, da tabbatar da moriyar kai da faduwar wani, yayin da ra’ayin da kasar Sin ke tsayawa a kai shi ne, barin bangarori daban daban su yi shawarwari, da tabbatar da moriyar dukkan bangarori, da neman ci gaban tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiya a lokaci guda. Ko shakka babu ra’ayin kasar Sin shi ne mai samun karbuwa da amincewa daga al’ummun duniya. (Bello Wang)

Amurka
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Dalilin Da Ya Sa Sabon Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Jihar Mongoliya Ta Gida Ke Jawo Hankalin Duniya

Dalilin Da Ya Sa Sabon Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Jihar Mongoliya Ta Gida Ke Jawo Hankalin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.