Bankin Stanbic na kasar Tanzania, daya daga manyan bankunan kasuwanci na kasar, ya kaddamar da tsarin biyan kudade ta amfani da kudin Sin RMB, tsarin da zai baiwa ‘yan kasuwar kasar damar saukaka gudanar da hada-hadar cinikayya da bangaren Sin. Karkashin tsarin, ‘yan kasuwa za su iya biya da karbar kudade kai tsaye ta amfani da RMB, wani mataki da ake sa ran zai rage tsadar hada-hadar biyan kudade da inganta cinikayya tsakanin kasashen biyu.
Da yake tsokaci dangane da hakan, mataimakin ministan raya masana’antu da cinikayya na Tanzania Dennis Londo, ya ce kaddamar da tsarin zai samar da wasu damarmaki ga ‘yan kasuwar Tanzania, ta yadda za su shiga karin kasuwannin kasa da kasa bisa managarcin yanayi.
Ministan ya kuma ce darajar hajojin Tanzania da ke shiga kasuwannin Sin ta karu daga dalar Amurka miliyan 442.96 a shekarar 2024 zuwa dala miliyan 512.6 a shekarar 2025, yayin da kuma darajar hajojin da kasar ke shigowa da su daga Sin ta karu daga dala biliyan 4.78 zuwa dala biliyan 5.64.
Ministan ya kuma ce wadannan alkaluma sun shaida muhimmancin da kasar Sin ke da shi a matsayin abokiyar huldar cinikayya, kuma tsarin biyan kudade ta amfani kai tsaye da RMB, zai iya rage dawainiyar canjin kudi ga ‘yan kasuwar Tanzania masu shigo da hajoji daga Sin, tare da baiwa masu fitar da hajojin kasar karin dama ta karbar kudaden cinikayya kai tsaye daga masu sayayya na Sin. (Saminu Alhassan)














