Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi afuwa ga fursunoni 27 da ke gidajen gyaran hali daban-daban a jihar Kaduna, domin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Nijeriya.
Wannan ya sa adadin mutanen da suka amfana da shirye-shiryen afuwar da gwamnatin gwamnan ta aiwatar tun bayan hawansa mulki ya haura 500.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar, Malam Ahmed Maiyaki, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.
Ya ce gwamnatin jihar ta kashe sama da naira miliyan 300 wajen biyan tarar wasu fursunoni da kuma diyya ga wadanda laifuka suka shafa tun bayan da Gwamna Uba Sani ya karbi mulki a watan Mayun 2023.
A cewarsa, matakin na daga cikin kokarin gwamnatin na tabbatar da tsarin adalci da ya hada da hukunta masu laifi, tare da ba wadanda suka cancanta damar gyara rayuwarsu da komawa cikin al’umma.
Shi ma Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Sir James A. Kanyip, ya ce gwamnan ya saba bayar da irin wannan afuwa a lokuta na musamman kamar Ranar Sabuwar Shekara, Ranar Dimokuradiyya da Ranar ’Yancin Najeriya.
Ya bayyana cewa ana gudanar da tsarin afuwar ne bisa ka’idojin da aka gindaya, tare da la’akari da gyaran hali, adalci da kuma hakkin wadanda lamarin ya shafa.
Kanyip ya ce biyan tara da diyya na taimakawa wajen cire matsalolin kudi da kan hana wasu fursunoni da suka cancanta samun damar fita daga gidan yari.
Ya kara da cewa ci gaba da aiwatar da shirin na nuna cewa afuwar ba wai wani abu ne da ake yi sau daya kawai ba, illa wani bangare ne na tsarin gwamnatin na inganta adalci da sake shigar da wadanda suka cancanta cikin al’umma.
Malam Ahmed Maiyaki ya sake tabbatar da kudurin gwamnatin Gwamna Uba Sani na kare al’umma da kuma mutunta muradun wadanda aka aikata wa laifi, tare da taimaka wa wadanda suka cancanta su koma ga iyalansu da al’ummominsu domin ci gaba da rayuwa a matsayin ’yan kasa masu amfani.












