ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, June 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Burina Shi Ne Na Zama ‘Celebrity’ Duk Duniya A San Ni

by Rabi'at Sidi Bala
3 months ago
Celebrity

Ci gaba daga makon jiya

Yau ma shafin na tafe da wata fitacciyar jarumar wato, HAJIYA ASIYA MUHAMMAD wacce aka fi sani da UWAR DASHI. Inda ta fayyacewa masu karatu zare da abawa na wasu abubuwan dake faruwa a cikin masana’antar Kannywood, kana fitacciyar jarumar ta yi wani kira ga masu yunƙurin shiga cikin masana’antar ta Kannywood, har ma da wasu batutuwan masu yawa da suka shafi rayuwarta da kuma sana’ar ta.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar Jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA kamar haka;

ADVERTISEMENT
  • Kotu Ta Yanke Wa Jarumar Kannywood Samha Hukuncin Ɗaurin Wata 6 A Gidan Yari
  • Na Yi Lokacin Da Idan Aka Gan Ni Ake Gudu A Masana’antar Kannywood – Mai Dawayya

Bayan ƙalubalen da ki ka fuskanta cikin masana’antar ko akwai wasu nasarori da ki ka samu game da fim?

Na samu nasara sosai, ko ba komai akwai alfarma, wanda wani idan na shiga Napep ɗinsa idan na ciro kuɗi zai ce “haba Mama ai mun sanki ni fans ɗinki ne, ba zan karɓi kuɗinki ba”. Akwai wanda na je ‘printing’ in a banza ne zan iya biyan wajen N6000, amma ya ce “Mama ni fans ɗinki ne ku bar shi kawai”. A haka ma fans ɗina za su kira ni “Momi ɗan turo account ɗinki”, kuma ban ma san ina suke samo Lamba ta ba. ‘Yar N1000, N2000, N3000, a turo min ace ga shi kya yi cefane. Wannan ai babbar nasara ce.

LABARAI MASU NASABA

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro

Ya Kamata Mawaƙa Su Guji Munafunci Da Hassada Su Rungumi Juna —Fati UK

Ko kina da ubangida a cikin masana’antar Kannywood?

Shugaba me kamfanin Kairiyya shi ne ubangidana, saboda shi ya bawa Auwalu Jauro damar ya kira ni. Duk wani aiki idan ya taso zai kira ni, kuma Alhmdulillahi har yanzu ina tare da shi Shugaba Mai khairiyya, akwai mutuntawa da girmamawa tsakanina da shi har gobe har jibi. Yana da ‘yancin ya ce yi kaza ki yi, bar kaza ki bari, gashi dai kusan nace na haife shi.

Ya ki ka ɗauki fim a wajenki?

Na ɗauke ta sana’a.

Mene ne burinki na gaba game da flm?

Burina shi ne na zama ‘celebrity’ duk duniya a sanni.

Bayan fim kina wata sana’ar ne?

Sana’o’i na kusan guda uku ne, ni ‘Women Leader’ ce a APC ta Rijiyar Lemo, wacce Buhari yayi ‘hand oɓer’ da sunanta a wurin Tinubu, ‘Women Leade’r ta ‘Word’ a yanzu haka. Na biyu ina siyar da Gado, Madubi, Kujeru, Katifu. Ba abin da ba na sayar wa, daga nan har sa’udiyya suna turo kuɗaɗensu ina siya musu shaddodi da atamfofi da lesussuka.

Ya alaƙarki take da sauran jarumai, da kuma waɗanda kuke tare da su tun kafin ki fara fim?

Alaƙata da sauran jarumai kyakkyawa ce, saboda duk duniya babu wani jarumi da zan ce ina jin haushinsa. Ni dai ba a taɓa nuna min ana jin haushina ba, ina da kyakkyawar alaƙa da kowa. Sai kuma sauran mutane kafin na fara fim, gaskiya na janyewa wasu jiki, waɗansu sun janye min jiki. Domin wasu mutane suna kallon duk ɗan fim ya zama ɗan iska, to ni kafin ka janye min ma nake janye maka. Saboda ina da zuciya ba na son ka faɗa min babu daɗi, duk sana’ar nan da nake yi abu ne me wahala ka ganni a gidanka. Shi ya sa nake zaune lafiya da kowa. Gidan da nake ciki tun ban fi ‘yar shekara ashirin ba na gina shi, kuma har yanzu a cikinsa nake, saboda na iya zama da mutane lafiya.

Ko akwai wani gyara ko cigaba da ki ke ganin ya kamata a kawo cikin masana’antar Kannywood?

Eh, akwai. Akwai baragurbi a ciki ‘yan fici-ficin yara, mutum yana da N110,000, sai ya ƙirƙiri yin fim ba dan komai ba saboda iya shege, da sakarci. To, ire-irensu dan Allah a riƙa bibiyar su in an kama su a ci uwarsu, saboda suna mantawa suna da ƙanne ko suna da ‘ya’ya wanda idan an yi musu haka ba za su ji daɗi ba. Mutum ‘yar dubunsa N110,000, N120,000 sai ya ƙirƙiri fim, fim ɗin a ƙirƙiri wani ƙauye ace na kwana ne. Yarinya ke kuma saboda kina kwaɗayin fim ɗin kina so lallai ke ma sai an fito da ke, sai su ɗebi ‘yan fici-ficin yara su tafi da su, ɗan fim bai kai ya kawo ba sai a yi kwana uku. A shiga ɗakuna da ‘ya’yan mutane a kwakkwana da su. Ƙauyen nan da suka je akwai mutane kuma suna kallon abin da ake yi, amma ba yadda za su yi, saboda wanda zai basu gidan nan ko ɗakin nan sai an sami wanda ya fi ƙarfin ‘yan unguwar. To, dan Allah so nake hukumar tace finafinai ta saka ido a kansu. Duk wanda aka je aka kamo da haka a hukunta su. Ƙauyuka-ƙauyuka suke bi, wannan dai shi ne dai gyaran, domin ɓatawa sana’ar fim suna suke yi, suna tashi magana cewa za su yi ‘yan fim daman ‘yan iska ne. wanda ba haka ake yi ba, ba kowa ne yake yin hakan ba.

 

Wacce shawara za ki bawa masu ƙoƙarin shiga masana’antar Kannywood?

Kina sha’awar fim to, ki kama kanki, ki san mutuncin kanki, ki yarda fim sana’a ce, kar ki banzatar da kanki. Domin sai ka banzatar da kanka kake zama ɗan banza, idan ka kama kanka za ka zama kamamme. Kuma idan ka kama kanka ka tsare mutuncinka ba mutumin da ya isa ya ce lallai sai ya taka ka. Harkar fim sana’a ce kuma ku ɗauke ta sana’a, idan ke yarinya ce ki fito da yardar iyayenki, idan ba su yarda ba ki yi haƙuri. Saboda idan ba su yarda ba ma, a banza ki zo, a banza za ki koma, ba tsiyar da za ki tsinana. Kuma idan aka baki rol ki ɗauke shi da gaske ne ba wai wasa bane. Idan kuma ke dattijuwa ce dan Allah ya ni ya ke bai kamata mu je cikin yara ko mu saki baki ko mu riƙa zancen banza da su, ko wani makamancin haka ba. Ko kuma yaro ya yi miki abu ki hau zaginsa, ba haka bane. Yana sane ya baro iyayensa ya zo, ke ma ki ka baro naki ‘ya’yan a can, idan kin ga ya yi ba daidai ba nasiha kawai ya kamata ki yi masa, ba ki riƙa ƙunduma masa ashar sai ka ce ke ki ka haife shi ba. Nan ma yana jaho raini yana jaho wulaƙanci.

 

Ko akwai wata shawara da za ki bawa sauran abokan sana’arki?

Eh, akwai. Shawara ga Daraktoci ko Furodusas, idan yarinya ta zo a ƙoƙarin son tayi fim, dan Allah ku riƙa yin haƙuri da halinta. Domin ita ma iyaye suna sonta ta bujire ta taho ta ce musu shi take so, dole suka yarda suka haƙura. Kuma ko ba komai kuma kuna da ‘ya’ya, idan ba ku da ‘ya’ya za ku yi nan gaba, ko kuna da ƙanne. A riƙa yin haƙuri da su ba wai a riƙa cewa “ai bata iya ba”, a riƙa kyararta ana hantararta da sauransu. A’a! ba haka bane ba, dan Allah a riƙa yin haƙuri da sababbin jarumai waɗanda suke shigowa mata ko maza. Kuma dan Allah idan mutum ya yi aiki a riƙa ƙoƙarin fita haƙƙinsa, idan kuma kuɗin da za a bashi tabbas bai kai ya kaho ba, to, tun kafin ya zo a gaya masa ga kuɗin da za a bashi, in ya ga ya yi masa sai ya zo ya yi. Idan ya ga bai yi masa ba ya ce bai yi masa ba, ku nemo wanda kuɗin ya yi masa, domin wani shi kyauta ma zai iya zuwa ya yi.

 

Me za ki ce da gidan jaridar Leadership Hausa?

Allah ya yi wa gidan jaridar Leadership albarka, Allah ya ɗaukaka ku, ya ƙara ɗaukaka ku. Allah ya tsare ku, ya tsare mutuncinku, Allah ya kare ku ya kare mutuncinku. Ubangiji ya ƙara muku daraja, Allah ya haskaka ku a idon duniya dan matsayin shugaba (s.a.w). Abin da yake kuskure ubangiji ya hane ku da faɗa, abin da yake daidai ubangiji Allah ya sa ku yi shi. Allah ya raya muku iyalinku, Allah yayi muku albarka, Allah ya sa ku gama da duniya lafiya alfarmar Muhammadur rasulullahi (s.a.w).

LEADERSHIP HAUSA! LEADERSHIP HAUSA!! Allah ya kare ki, Allah ya ɗaukaka ki, Allah ya haskaka ki.

 

 

Celebrity
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ban Sha Wata Wahala Ba A Gwagwarmayar Shiga Harkar Fim —Hadiza
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Hotunan Ango Da Amarya Kafin Daura Aure

MASU ALAKA

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro
Nishadi

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro

May 31, 2026
Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Nishadi

Ya Kamata Mawaƙa Su Guji Munafunci Da Hassada Su Rungumi Juna —Fati UK

May 23, 2026
Har Yanzu Burina Bai Cika Ba A Waka —Hadiza Maikano
Nishadi

Har Yanzu Burina Bai Cika Ba A Waka —Hadiza Maikano

May 16, 2026
Next Post
Binciken CGTN: Galibin Amurkawa Na Ganin Darajar Dangantaka Mai Karko Da Sin

Binciken CGTN: Galibin Amurkawa Na Ganin Darajar Dangantaka Mai Karko Da Sin

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Wannan Hakki Na Tushe Yana Da Matukar Muhimmanci

Wannan Hakki Na Tushe Yana Da Matukar Muhimmanci

June 13, 2026
An Cafke Mutum Uku Kan Kisan Mawaki Dan Asalin Nijeriya Da Birtaniya

An Cafke Mutum Uku Kan Kisan Mawaki Dan Asalin Nijeriya Da Birtaniya

June 13, 2026
Allah Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Matawalle

Allah Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Matawalle

June 13, 2026
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

’Yansanda Sun Cafke Mutun Biyu Da Ake Zargi Da Fashi Da Makami A Adamawa

June 13, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Kaddamar Da Tsarin Fasahar Zamani (AI) Domin Inganta Tsaro Da Harkar Sufuri

Kamfanin Simintin Dangote Ya Kaddamar Da Tsarin Fasahar Zamani (AI) Domin Inganta Tsaro Da Harkar Sufuri

June 13, 2026
Tsohon Kakakin Ma’aikatar Tsaro Rabe Abubakar Ya Rasu A Hannun ‘Ƴan Bindiga

Tsohon Kakakin Ma’aikatar Tsaro Rabe Abubakar Ya Rasu A Hannun ‘Ƴan Bindiga

June 13, 2026
Yadda Matata Ta Daina Girki, Ta Ke Lakaɗamin Duka — Miji Ya Koka

Yadda Matata Ta Daina Girki, Ta Ke Lakaɗamin Duka — Miji Ya Koka

June 13, 2026
Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamna Uba Sani Ya ‘Yanta Fursunoni 97

Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamna Uba Sani Ya ‘Yanta Fursunoni 97

June 13, 2026
Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata

Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata

June 13, 2026
Hukumar FAO Ta Samar Da Shirin Kiwon Tarwada A Jihar Gombe

Hukumar FAO Ta Samar Da Shirin Kiwon Tarwada A Jihar Gombe

June 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.