ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cin Amana Uku Da Suka Sauya Tarihi A Duniya

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
7 months ago
Cin amana

Tarihi na dauke da labarin maciya amana da masu goyon baya da kuma ‘yan ba ruwanmu.

A lokuta da dama cin amana na kawo sauyi cikin wasu tsare-tsare.

BBC ta kawo misalin irin wadannan cin amana: Daya daga ciki ne ya yi sanadiyyar hamBarar da mulkin wani babban sarki.

ADVERTISEMENT

Akwai kuma cin amanar da ya yi sanadin kashe wani fitattacen jagoran al’ummar Rum.

Yayin da cin amana na uku ya bayar da gudummawa waje samun nasara a yakin Birtaniya da Amurka.

LABARAI MASU NASABA

Tarihin Shugaban Makaranta Na Farko A Arewa Hedimasta (2)

Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959. (2)

 

Julius Caesar: Taka-tsantsan da makusanta

Cin amanar da aka yi wa Julius Ceaser ranar 15 ga watan Maris shekara ta 44 kafin haihuwar Annabi Isa (A.S) ta sauya tsarin Rum.

Jinjina ga marubuci William Shakespear wanda ya yi amfani da kalmar Beware of The Ideas of March’ watau ka yi taka-tsantsan da mutanen da ke kusa da kai.

Abin da ha kan ya ke nufi shi ne ranar 74 a kalandar Rum ita ce dai dai da ranar 15 ga watan Maris kuma ranar da aka ci amanar Julius Ceaser.

Julius Ceaser ya kasance Janar na Soja kuma mai fada a ji a kasar Rum. A shekara ta 44 kafin haihuwar Annabi Isa ya ayyana kansa a matsayin mai mulkin kama-karya na dindindin.

Abin da ke nufin shi kadai zai mulki Kasar Rum.

Makiyansa a siyasa sun yi fargabar zai iya yin karfi sosai abin da ya sa suka dauki alwashin hamBarar da shi.

Jagorori uku Marcus Junius Brutus da Gaius Cassius Longinus da kuma Decimus Junius Brutus dukkansu sanatoci ne a majalisa.

Decimus Brutus ya fi kowa kusanci da Caesar har ma yana tunanin shi zai gaje shi. Amma Marcus Brutus yana adawa da Caesar – kuma sun fafata a ya kin Battle of Pharsalus a shekara ta 48 daga baya Ceaser ya yi masa afuwa har ma ya kara masa girma.

Su ukun tare da wasu mutum 60 ne suka yi wa Caesar kawanya a zauren majalisar dattawa kuma suka kashe shi.

Ba za mu iya cewa ga wasiyyar Caeser ta karshe ba, amma marubuci Shakespeare ya bayyana tsananin cin amanar a wasan kwaikwayon da ya rubuta mai tarihi.

A ciki Julius Caesar ya tambayi Marcus Brutus “har da kai Brutus?”, – hakan na nufin bai yi zaton mutumin da ya yi wa afuwa kuma ya karawa girma har ya dauke shi a matsayin aboki zai ci amanarsa ba.

Sai dai wadanda suka ci amana tare da kashe Ceaser sun manta matsayinsa da kuma irin farin jinin da Ceaser ke da shi wurin al’umma.

Yayin da suka sanar da mutuwarsa a zauren Capitoline Hill da ke Rum sai jama’a suka yi tsit kowa ya yi shiru daga nan kuma sai wuri ya yamutse inda aka kori Marcus Brutus da Decimus Brutus da kuma Cassius daga gari.

Mutuwar Ceaser ce ta kawo karshen mulkin Rum, daga nan sai Gaius Julius Caesar OctaBianus Augustus ya zama Sarkin Rum na farko.

 

Sarauniya Isabella ta Faransa

Yayin da sarauniyar farko ta bayyana a Biritaniya a karni na 16, akwai sarakuna mata da suka yi fice a tarihi.

Daya daga ciki ita ce Isabella ‘yar Faransa wacce ake kira “She-Wolf of France,” ta taka muhimmiyar rawa wajen kashe Sarki Edward II na Ingila a shekara ta 1327.

‘Yar Sarkin Faransa Philip IB an haife ta a farkon shekara ta 1290 ta auri Edward ranar 25 ga Janairu1308.

Edward ya shahara cikin manyan mutane, na farko Piers Gaveston wanda aka kama kuma aka kashe shi a watan Yuni 1312 da manyan mutane da aka samu da laifi, akwai kuma Hugh Despenser.

Lokacin da Edward ya ce zai yaki Isabella.

Despenser ya zarge ta leken asiri don haka ya kwace kadarorinta kuma ya hana ta ganin mijinta.

Duk da cewar Edward ya yi niyyar aiken ta Faransa don tattaunawar sulhu da dan uwanta.

Edward ma na son ziyartar Charles IB a Faransa amma ba ya son barin Ingila saboda barazanar da ‘yan tawaye suka yi masa tare da Despenser.

Maimakon haka sai ya tura dansa kuma mai jiran gado.

Issabella ta samu kanta karkashin kulawar dan uwanta.

Ta yi amfani da karfin ikon da take da shi wajen bai wa sarki zaBi. Isabella da yarima mai jiran gado za su koma idan aka sauke Despenser daga mulki kuma aka mayar mata da kadarorinta da matsayinta, amma Edward ba shi da niyyar amincewa da bukatarta.

Isabella ta hada kai da Roger Mortimer, wani dan Ingila da ya yi gudun hijira bayan ya yi wa Sarki tawaye inda suka kulla yadda za su kutsa Ingila su hamBarar da sarki daga mulki.

Sun yi amfani da kudade da makaman da suka samu daga Belgium wajen kutsawa Ingila ranar 24 ga watan Satumban shekara ta1326.

Sarki Edward ya rasa magoya baya abin da ya sa Isabella ta kara samun hadin kai daga ‘yan uwan sarkin da danginsa.

An kama Hugh Despenser an kashe shi yayin da aka sauke Edward daga mulki sannan aka kashe shi a Berkeley Castle daga baya.

Sarki Edward na III ya fara mulki a irin ranar da aka yi auren iyayensa da ke rikici da juna, ranar 25 ga watan Janairun shekara ta 1327 .

 

Benedict Arnold: Babban mai cin amana a Amurka

A Amurka sunan Benedict Arnold daidai ya ke da cin amana. Ya kasance jarumi a wurin George Washington saboda ya taimaka wa Amurka ta samu nasara a yakin Fort Ticonderoga cikin watan Mayu a shekara ta 1775

Ya samu karin nasara a yakin Saratoga a shekara ta 1777, lamarin da ya sanya Faransa hada kai da masu juyin juya hali, sai dai lamari ya sauya daga baya bayan Arnold ya ci amanar Amurka ta hanyar fara yiwa Birtaniya leken asiri.

Arnold na ganin Amurka ba ta biya shi yadda abin da ya kamata ba kuma an fifita wasu mutane akansa.

Almubazzarancin matarsa ya sa shi cin bashi har Washington ta zarge shi da karya doka Lamarin da ya Bata masa rai, ga bashi ya yi masa yawa daga nan sai ya kulla alaka da Birtaniya.

Da Washington ta ba shi kwamandan sojoji a shekara ta 1780.

Sai Arnold ya dage zai shugabanci tsaro a West Pont da New York da kuma kogin Hudson. Yankuna ne masu muhimmanci a harkokin sadarwa da sufuri.

Ya yi shirin ragewa yankin karfin tsaro sannan ya mikawa Birtaniya wadda za ta ba shi fan 20,000 tare da yiwuwar yaudarar Washington ta fada hannun abokan gaba.

An bankado shirin Arnold ne sakamakon kama wani jami’in leken asirin Birtaniya kuma abokin Arnold da wasu takardu. Amma ya yi sa’ar tserewa inda ya shiga jirgin yakin Birtaniya mai suna HMS Bulture.

An yi masa karin girma zuwa Birgediya Janar daga nan kuma ya fara yakar tsoffin iyayen gidansa.

Ya koma Ingila da zama har ya mutu a shekara ta 1801.

Cin amana
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas
Cin amana
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Tarihi

Tarihin Shugaban Makaranta Na Farko A Arewa Hedimasta (2)

May 30, 2026
Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959
Tarihi

Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959. (2)

January 11, 2026
Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959
Tarihi

Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959

January 4, 2026
Next Post
Darussa Daga Ramadan Na (1)

Darussa Daga Ramadan Na (4)

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.