ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Darussa Daga Ramadan Na (4)

by Nuhu Ubale Ibrahim
7 months ago
Darussa

A cikin watan Ramalana muna koyon nisantar algus da yaudara, domin muna tuna cewa Allah Maɗaukaki Yana kallon mu a kowane lokaci. Ba don tsoron mutane muke barin ci da sha da rana ba, domin da ba don girman Allah da lura da kallonsa ba, da mutum zai iya ci ko ya sha a ɓoye ba tare da wani ya sani ba. Amma muminin gaske yana barin hakan ne saboda ya san Allah na ganin sa.

Wannan matsayi shi ake kira Ihsani, watau kai ibada da cikakken sanin cewa kana ƙarƙashin kulawar Allah Yana ganinka. Manzon Allah (S.A.W) ya bayyana ma’anar Ihsani a cikin hadisin da ya zo a cikin Sahihul Bukhari da Muslim, inda ya ce:
“Ihsani shi ne: ka bauta wa Allah kamar kana ganin Sa; idan kai ba ka ganin Sa, to, Shi Yana ganin ka” Wannan kalma ta ƙunshi asalin gyaran zuciya da tsarkake niyya. Ihsani ba wai kawai yawan ibada ba ne, sai dai ingancinta da tsarkinta ya tattare da ita. Yana nufin ka yi salla da natsuwa, ka yi azumi da gaskiya, ka yi addu’a da tawali’u, ka kuma nisanci saɓo ko da babu mai ganin ka.

  • Darussa Daga Ramadan Na (1)
  • Darussa Daga Ramadan Na (2)

Ramalana wata ne da ke horar da zuciya a kan wannan matsayi. Domin azumi ibada ce ta sirri; babu wanda ya san ko mutum ya karya azuminsa, sanin haka sai shi da Ubangijinsa. Wannan sirrin yana gina wa mumini jin tsoron Allah da kiyaye dokokinsa a fai da ɓoye, da ganin girmansa a zuciya.

ADVERTISEMENT

Idan wannan darasi ya zauna a zuciya, to ba a cikin Ramalana kaɗai zai canza bawa ba, har rayuwar mutum baki ɗaya za ta canza. Zai nisanci algus a kasuwanci, zai guji ha’inci a amanar da aka ɗora masa, zai bar kallon haram da sauraron abin da bai halatta ba, domin ya san cewa Allah na ganin sa.

Ihsani shi ne ginshiƙin kamala a addini. Shi ne mataki mafi girma bayan Musulunci da Imani. Duk wanda ya kai wannan matsayi, zuciyarsa tana rayuwa cikin kulawar Allah, ayyukansa suna cike da tsari da ladabi, rayuwarsa kuma tana cike da haske.

LABARAI MASU NASABA

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

Saboda haka, Ramalana makaranta ce ta Ihsani. Duk wanda ya koyi darasin nan da gaske, zai fita daga watan nan yana da sabuwar zuciya mai cike tsoron Allah, mai ƙaunar Sa, mai jin daɗin ibada, mai nisantar algus a fili da a ɓoye.

Allah Ya sanya mu cikin bayinsa masu Ihsani, Ya tsarkake zukatanmu, Ya karɓi ibadunmu. Amin.

Darussa
Nuhu Ubale Ibrahim
+ postsBio
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 23
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 22

MASU ALAKA

Darussa
Ilimi

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

August 31, 2026
Darussa
Ilimi

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

August 29, 2026
Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa
Ta’aziyya

Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

August 2, 2026
Next Post
An Nuna Shagalin CMG Na Murnar Bikin Bazara A Jiragen Kasa Na Nijeriya

An Nuna Shagalin CMG Na Murnar Bikin Bazara A Jiragen Kasa Na Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.