Majalisar Dokokin Jihar Kano ta buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta ɗaukar mataki kan ɓarkewar cutar mashaƙo biyon bayan kashe yara sama da 50 a Karamar Hukumar Rano.
An ce cutar ta fi ƙamari a garuruwan Ridin da Sabuwar Kaura.
‘Yan majalisar sun kuma ce cutar ta yaɗu zuwa wasu yankuna a Ƙaramar Hukumar Kiru da ke maƙwabtaka da Rano.
Gwamnati ta riga ta samar da magunguna tare da tura jami’an lafiya zuwa yankunan da abin ya shafa, amma ‘yan majalisar sun ce ana buƙatar ƙarin tallafin gaggawa.
Majalisar ta kuma buƙaci gwamnati ta ƙara yawan rigakafi da sauran matakan kariya domin hana cutar yaɗuwa zuwa wasu yankuna.
Daga bisani, majalisar ta umarci Kwamitinta na Lafiya da ya haɗa kai da Ma’aikatar Lafiya domin samar da tallafin gaggawa tare da tabbatar da ɗaukar matakan da suka dace wajen shawo kan cutar.














