Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasa ta Sin, Chen Xi, ya bayyana a yau Jumma’a cewa, dakarun sojin saman kasar Sin da na Masar za su gudanar da atisayen hadin gwiwa a kasar Masar daga tsakiyar watan Agusta zuwa farkon watan Satumba.
Jami’in ya shaida wa taron manema labarai cewa atisayen, wanda aka yi wa lakabi da “Mikiyoyin wayewar kai na 2026” ko “Eagles of Civilization-2026”, shi ne atisayen hadin gwiwa na biyu tsakanin dakarun sojin sama na kasashen biyu.
Chen ya kuma ce atisayen na hadin gwiwa, zai kara inganta aminci da abota ta gargajiya, da zurfafa hadin gwiwa tsakanin rundunonin sojin biyu, da kuma taimaka wa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














