ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matashi Ya Shiga Hannu Kan Zargin Wulaƙanta Alƙur’ani A Kebbi

by Umar Faruk
4 weeks ago

Rundunar ’Yansandan Jihar Kebbi ta kama wani matashi mai shekaru 29, Abubakar Musa, bisa zargin haɗa baki da wasu mutane wajen wulaƙanta Alƙur’ani Mai Girma a Ƙaramar Hukumar Zuru.

Ana zargin Musa, wanda ke zaune a ƙauyen Rafin Mose da ke Zuru, da haɗa baki wajen aikata laifuka da suka haɗa da wulakanta Alƙur’ani, aikata tsafi da kuma ayyukan da ka iya haifar da tashin hankali a tsakanin al’umma.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau, ta ce lamarin ya faru ne ranar 9 ga watan Agusta, 2026, da misalin ƙarfe 7 na dare.

ADVERTISEMENT

Rundunar ta ce bincike ya nuna cewa Musa ya haɗa baki da wasu mutane biyu, Rabi’u Tela, mijin Zarau Hassan, da Hamza Zango, inda suka tono wani rami a cikin ɗakin Zarau Hassan.

A cewar ’yansandan, an binne wani Alƙur’ani a cikin ramin tare da wasu abubuwa da suka haɗa da maniyyi, goro fari da ja, kayan cikin dabbobin da suka mutu da sauran abubuwan da ake zargin na tsafi ne.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Rundunar ta ce ana zargin an aikata hakan ne domin sanya Zarau Hassan ta zama mai biyayya ga mijinta, Rabi’u Tela.

Ta kuma ce irin wannan aiki na iya haifar da fitina da kawo cikas ga zaman lafiya tsakanin al’ummar Musulmi a yankin.

A halin yanzu, ’yansanda na neman Rabi’u Tela da Hamza Zango, waɗanda ake zargi da hannu a lamarin kuma duk sun tsere.

Rundunar ta ce Abubakar Musa yana hannun ’yansanda, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.

Kwamishinan ’Yansandan Jihar Kebbi, CP Umar M. Hadejia, ya yi Allah-wadai da lamarin.

Ya bayyana cewa rundunar za ta ɗauki matakin da ya dace bisa doka kan duk wanda ayyukansa za su kawo cikas ga zaman lafiya, tsaron jama’a da haɗin kan al’umma.

Umar Faruk
+ postsBio
  • Umar Faruk
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk/
    Gwamnatin Kebbi Ta Amince Da ₦2.07bn Alawus-alawus Ga Ma’aikatan Manyan Makarantu
  • Umar Faruk
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk/
    Gwamnan Kebbi Ya Maye Gurbin Mataimakinsa Da Ibrahim Augie A Zaɓen 2027
  • Umar Faruk
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk/
    Gwamnan Kebbi Ya Miƙa Yara 5 Da Aka Ceto Daga Hannun Masu Safarar Mutane Ga Iyayensu
  • Umar Faruk
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk/
    Arangama Ta Yi Sanadin Mutuwar ‘Yan Bindiga 17 Da ‘Yansanda 10 A Kebbi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Sin Ta Yi Gargadi Kan Sake Farfado Da Karfin Sojin Japan Gabanin Ranar Tunawa Da Mika Wuyanta A Yakin Duniya Na II

Sin Ta Yi Gargadi Kan Sake Farfado Da Karfin Sojin Japan Gabanin Ranar Tunawa Da Mika Wuyanta A Yakin Duniya Na II

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.