Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya yi kira ga jami’an ‘yan sandan kasar da su ci gaba da dukufa ga hidimta wa jama’a, da kasancewa amintattun masu ba da kariya na jam’iyya da kuma al’umma, tare da nuna cikakkiyar himmar sauke nauyi da nuna sadaukarwa ga ayyukansu.
Xi, wanda har ila yau shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta Sin (JKS) kuma shugaban hukumar soji ta tsakiya, ya bayyana hakan ne a cikin wata wasikar bayar da amsa da ya aika wa rundunar ‘yan sanda ta matakin farko a birnin Zhangzhou, da ke lardin Fujian na gabashin kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
ADVERTISEMENT