Hukumar Tsaro ta NSCDC ta kama wasu mutane da ake zargi da hannu a satar motoci, fashi da makami, satar wayoyin wutar lantarki da wasu laifuka a Abuja da jihohin da ke maƙwabtaka da ita.
Hukumar ta gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatarta da ke Abuja, bayan gudanar da samame bisa bayanan sirri.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama shi ne Adam Yusuf, wanda hukumar ta ce memba ne a wata ƙungiyar masu satar motoci da ke aiki a jihohi daban-daban.
An kama shi ne a ƙarƙashin gadar Mpape lokacin da ake zargin yana ƙoƙarin kai wata mota ƙirar Toyota Camry da aka sace.
NSCDC ta kuma ƙwato bindiga ƙirar AK-47, harsasai 16 da Naira 70,000 daga hannun wasu da ake zargi da hannu a fashi da makami.
Sauran waɗanda aka kama sun haɗa da waɗanda ake zargi da satar wayoyin wutar lantarki da kuma wani mutum da ake zargin ya saci batir 15 na manyan motoci.














