ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 22, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilin Dawowar Kayayyakin Tarihi Gida Shi Ne Ci Gaban Kasashe Masu Tasowa

by Sulaiman and CGTN Hausa
5 months ago
Tarihi

A shekarun nan, a kan ga yadda wata kasa da ta taba yin mulkin mallaka ke mayar da wasu kayayyakin tarihi da ta kwace a baya ga kasashensu na asali.

Kana a kwanan nan, majalisar wakilai ta kasar Faransa ta zartas da wata dokar da za ta saukaka aikin mayar da kayayyakin tarihi da kasar ta kwace daga kasashen da ta taba yi wa mulkin mallaka.

To, duk wadannan ci gaban da aka samu, dalilin su shi ne wani yanayin da ake ciki, na haskakawar tauraron kasashe masu tasowa.Bari mu dauki kasar Faransa a matsayin misali.

ADVERTISEMENT

Da ma kasar ta gabatar da dimbin dokoki don hana mayar da kayan tarihi ga sauran kasashe. Sai dai a wannan karo ta nuna sassauci. Saboda me? Saboda kasar na neman daidaita huldarta da wasu kasashen dake nahiyar Afirka, musamman ma kasashen Mali, da Burkina Faso, da kuma Nijar.

Ta haka muna iya ganin cewa, dawowar kayayyakin tarihi kasashensu na asali ta shafi daga matsayin wadannan kasashen. Ban da haka, ta kuma shafi kokarin da kasashe masu tasowa suke don ganin a mayar musu da kayayyakin tarihi da aka kwace daga hannunsu.

LABARAI MASU NASABA

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Misali, mun san a Najeriya, an fara neman a dawo da kayayyakin tarihi tun kafuwar kasar a shekarar 1960. Kana a shekarar 2007, an kafa Tawagar Tattaunawa Ta Benin don tattauna batun mayarwa Najeriya da kayayyakin tarihinta masu alaka da al’adun daular Benin. Kana a shekarar 2022, kasar Jamus ta mika ma kasar Najeriya wasu kayayyakin tagulla guda 1130. Kafin daga bisani kasar Holland ta mayarwa Najeriya da kayayyakin tagulla 119 a shekarar 2025.

A nata bangare, kasar Sin ita ma ta yi matukar kokari don neman dawo da kayayyakin tarihinta da aka kwace gida, inda dabarun da ta dauka suka hada da tattauawar jami’ai masu kula da aikin hulda da sauran kasashe, da karfafa hadin gwiwar kasashe daban daban, da dai sauransu.

An ce, tun daga kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949 har zuwa yanzu kasar ta riga ta dawo da kayayyakin tarihi fiye da dubu 150 cikin gidanta.

Ko da yake aikin neman dawo da kayayyakin tarihi gida yana da wahala sosai, amma su kasashe masu tasowa ba su taba yafe damar yin haka ba. Saboda me? Saboda dole sai an dawo da kayayyakin tarihi masu daraja da ’yan mulkin mallaka suka kwace, sa’an nan za a iya daidaita kura-kuran da aka yi a baya, da tabbatar da adalci a duniya.

Na biyu, shi ne domin kayan tarihi na dauke da tunani mai muhimmanci da ya shafi wata al’umma, don haka ta hanyar dawo da shi za a samu damar karfafa tushen ci gaban harkoki masu alaka da al’adun wata kasa.

Ban da haka, dalili na uku shi ne, yadda hasken kasashen yamma ya dishe ya sa su kasa kiyaye wadannan kayayyakin tarihi yadda ya kamata. Misali a shekarar 2023, cibiyar adana kayayyakin tarihi ta “The British Museum” ta kasar Birtaniya ta sanar da cewa, kayayyakin tarihi kimanin 2000 da ta rike, ciki har da dimbin kayayyakin da aka kwace daga kasashen Afirka, sun bace, ko an sace su, ko kuma sun lalace.

Sa’an nan bisa ra’ayin kasar Sin, yadda ake dawo da kayayyakin tarihi kasashensu na asali zai karfafawa kasashen gwiwa, don su gudanar da nazari da gadon al’adun gargajiya, da samun damar zamanantar da al’umma ta wata hanyar da ta dace da yanayin da suke ciki. (Bello Wang)

Tarihi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    NLC Ta Goyi Bayan Buƙatar Albashi N500,000 Da Rage Farashin Mai Zuwa N500
  • Sulaiman
    NSCDC Ta Kai Samame Masana’antar Lemo Da Ke Amfani da Gurɓatattun ’Ya’yan Itace A Legas
  • Sulaiman
    An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York
  • Sulaiman
    Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu
Tarihi
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
     Li Qiang Ya Gana Da Shugaban Kungiyar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Da Babban Jami’in Gudanarwarta
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ko Wadanne Gudanmawa Manufar Gaggauta Cinikayyar Waje Ta Sin A Fannin Hajojin Dakile Sauyin Yanayi Ka Iya Samarwa Duniya?

MASU ALAKA

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka
Ra'ayi Riga

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

September 14, 2026
Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Next Post
‘Yan Wasa 10 Da Ba Za Su Buga Gasar Kofin Duniya Ba Sakamakon Rauni

'Yan Wasa 10 Da Ba Za Su Buga Gasar Kofin Duniya Ba Sakamakon Rauni

LABARAI MASU NASABA

 Li Qiang Ya Gana Da Shugaban Kungiyar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Da Babban Jami’in Gudanarwarta

 Li Qiang Ya Gana Da Shugaban Kungiyar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Da Babban Jami’in Gudanarwarta

September 22, 2026
Hare-hare: Ƙungiyar Kiristocin Arewa Ta Yi Gargaɗin Ka Da A Saba Da Kisa A Nijeriya

Hare-hare: Ƙungiyar Kiristocin Arewa Ta Yi Gargaɗin Ka Da A Saba Da Kisa A Nijeriya

September 22, 2026
Mutuwar Masu Haƙar Ma’adanai: Gwamnati Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Binciki Lamarin

Mutuwar Masu Haƙar Ma’adanai: Gwamnati Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Binciki Lamarin

September 22, 2026
Mun Kaɗu Matuƙa Kan Labarin Mutuwar ‘Yan Mauludi A Hanyar Saminaka – Gwamnan Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan 3.659 Ga ‘Yan Fansho

September 22, 2026
NLC

NLC Ta Goyi Bayan Buƙatar Albashi N500,000 Da Rage Farashin Mai Zuwa N500

September 22, 2026
Efcc

Dangote Ya Shirya Zuba Dala Biliyan 10 A Ɓangaren Wutar Lantarki

September 22, 2026
Kamfani A Kano Ya Miƙa Wa KCPC Kayayyaki Na ₦28.6m Da Amincinsu Ke Dab Da Ƙarewa

NSCDC Ta Kai Samame Masana’antar Lemo Da Ke Amfani da Gurɓatattun ’Ya’yan Itace A Legas

September 22, 2026
An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York

An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York

September 21, 2026
Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu

Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu

September 21, 2026
Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya

Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya

September 21, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.