ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Wasa 10 Da Ba Za Su Buga Gasar Kofin Duniya Ba Sakamakon Rauni

by Sulaiman and Rabilu Sanusi Bena
5 months ago
Kofin Duniya

Yayinda babbar gasar kofin Duniya ta bana da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da Canada ke karatowa, akwai manyan yan wasan kwallon kafa da kasashensu sun samu nasarar tsallakawa zuwa gasar amma Ba za su samu damar zuwa ba sakamakon raunin da suka samu, da yake dai zuwa yanzu kasashen basu fitar da jerin yan wasan da zasu wakilcesu ba amma dai akwai wadanda ko an fitar da sunayensu Bazasu samu damar zuwa ba:

Samu Aghehowa (Spain)

Dan wasan gaban Fc Porto Samu Aghehowa ya samu rauni a gwuiwarsa a watan Fabrairu, dan wasan mai shekaru 21, yana daga cikin yan wasa masu zafin nama wajen zura kwallaye da ake ganin zai iya taimakawa tawagar kasar Spain a kokarinta na ganin ta lashe gasar Kofin Duniya.

ADVERTISEMENT

Patrick Agyemang (Amurka)

An cire dan wasan gaban na Amurka daga wasan da ya bugawa Derby County bayan raunin da ya samu a wasan, Agyemang na daga cikin yan wasanda ke karawa tawagar Amurka kwarin gwuiwa a wasanninsu na baya, raunin da ya samu ya zama tamkar koma baya ga tawagar Amurka wadda Mauricio Pochettino ke jagoranta.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

Valentin Carboni (Argentina)

Dan wasan tsakiya Valentin Carboni, wanda yanzu haka ke zaman aro a kungiyar Racing, ya ji rauni a gwuiwarsa a watan Fabrairu, wanda hakan ya kawo karshen fatansa na shiga tawagar Argentina, dan wasan mai shekaru 21 ya riga ya samu damar buga wasa tareda manyan yan wasan tawagar ciki har da kyaftin din tawagar Lionel Messi.

Cameron Carter-Vickers (Amurka)

Dan wasan baya Cameron Carter-Vickers har yanzu akwai shakku dangane da zuwansa gasar kofin Duniya ta bana, bayan an yi masa tiyata a farkon kakar wasar bana, duk da cewa bai yanke tsammani gaba daya ba, damarsa ta wakiltar Amurka ta ragu sosai.

Hugo Ekitike (Faransa)

Dan wasan gaba na Liverpool Hugo Ekitike ya samu rauni a jijiya a wasan da Liverpool tayi rashin nasara a hannun PSG a gasar Zakarun Turai, raunin da ya samu zai yi sanadiyar da ba zai buga wani mummunan rauni da ya hana shi shiga gasar Faransa.

Juan Foyth (Argentina)

Dan wasanda ya lashe gasar cin kofin Duniya tareda Argentina a shekarar 2022 Juan Foyth ya samu rauni a gwuiwarsa a watan Janairu yayin da yake bugawa Villarreal wasa, dan wasan bayan zai rasa damar sake wakiltar Argentina a matakin gasar cin kofin Duniya.

Luis Ángel Malagón (Mexico)

Mai tsaron ragar kasar Mexico Luis Ángel Malagón yana murmurewa daga raunin da ya samu, idan bai murmure ba zuwa karshen kakar wasa ta bana hakan zai yiwa tawagar kasar Mexico mummunar illa a shirinta na tabuka abin azo a agani yayinda suke shirin karbar bakuncin gasar.

Joaquin Panichelli (Argentina)

An cire Joaquin Panichelli daga wasan da kungiyarsa ta Strasbourg ta samu nasara bayan ya samu rauni a karo na biyu cikin shekaru biyu, wannan koma-baya ya kawo karshen fatansa na shiga cikin tawagar Argentina ta gasar cin kofin Duniya.

Rodrygo (Brazil)

Tauraron Brazil Rodrygo Kuma dan wasan Real Madrid ba zai buga gasar ba yayinda yake kan murmurewa daga raunin da yake fama dashi, rashinsa babban rashi ne ga tawagar kasar Brazil wadda ke fatan cigaba da zama a matsayi na farko a jerin kasashen da suka fi lashe gasar a tarihi.

Mohammed Salisu (Ghana)

Dan wasan baya na Ghana Mohammed Salisu yana fuskantar yiwuwar rashin wakiltar kasarsa ta Ghana yayinda yake fama da jinya bayan raunin da ya samu a kafarsa a watan Janairu, wanda hakan ya sa ba zai buga wa Ghana wasa ba.

Kofin Duniya
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
Kofin Duniya
Rabilu Sanusi Bena
+ posts Bio
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Za’a Dakatar Da Wasa A Farkon Minti 10 Na Kowane Wasa A Kasar Argentina Saboda Girmama Messi
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Chelsea Ta Kammala Ɗaukar Ahanor Kan Fam Miliyan 40

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
Darajar Masana’Antar Manhajoji Ta Kasar Sin Na Iya Zarce Yuan Tiriliyan 20

Darajar Masana'Antar Manhajoji Ta Kasar Sin Na Iya Zarce Yuan Tiriliyan 20

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.