ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, September 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Labarin Lu Rongjie: Misalin Demokradiyya Da Shugabanci Mai Hidimtawa Al’umma

by CGTN Hausa and Sulaiman
3 months ago
Lu

Labarin Lu Rongjie, jami’in JKS na kauyen Miaojia na lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin da na gani a shafin jaridar intanet ta People’s Daily Online, ya tuna min da irin tsokacin da na gani a shafin sada zumunta na Facebook, bayan na wallafa wani bidiyon kauyen Caoba na gundumar Yang ta lardin Shaanxi, wadanda ke cewa, “ wannan kam ai ya girmi kauye, gwanin sha’awa” “…ki daina cewa kauye, sai ki ce kauyen birni” “yanzu nan kauye ne” da sauran makamantansu.

Irin wadannan tsokacin sun nuna irin koma bayan da har yanzu muke fama da su a yankuna da kasashenmu. A cikin ziyarce-ziyarcen da na yi a kasar Sin daga kauyuka zuwa garuruwa da manyan birane masu matukar ci gaba, yankunan kauyuka sun fi jan hankalina saboda irin ci gaban da nake ganin sun bambanta karara da abun da na saba gani.

A kauyukan kasar Sin ne za ka ga tituna da wutar lantarki tsawon sa’o’i 24 ba tare da katsewa ba, a kauyukan kasar Sin ne za ka ga sadarwar intanet da ruwan famfo sabanin abun da na saba gani a gida. A kauyukan kasar Sin ne za ka ga na’urar sanyaya wuri watau AC wadda a kasata, ko a birane, sai gidan wane da wane. A kuma kauyukan kasar Sin ne za ka ga yadda jami’ai da al’umma suka jajirce wajen yaki da talauci.Ko me ye dalilin irin wannan ci gaba da ake gani a kasar Sin? Dalilin ba ya rasa nasaba da salon shugabanci, karkashin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin wadda aka kafa ta yau shekaru 105 da suka gabata, kuma misalin shi ne jami’in jami’iyyar na kauyen Miaojia na lardin Zhejiang. Rohotanni sun bayyana cewa, mutanen kauyen ba sa kiran Lu Rongjie da sunansa, sai dai jami’in jam’iyya mai “takalman gudu,” saboda yadda yake a tafe a ko da yaushe muddun ba ya zaune a ofishinsa. Ya kan zagaye kauyen domin tattaunawa da mu’amala da jama’a saboda ya ji irin matsaloli da korafinsu ta yadda za a shawo kansu tun kafin su yi girma.

ADVERTISEMENT

Daga inda na fito, abu ne mai wuya a samu dan siyasar da ke zagaya al’ummarsa don sanin matsalolinsu, wakiltar jama’a ya zama tamkar wani aiki na karawa kai da makusanta karfi, haka kuma ya zama tamkar wani tikitin yawace-yawacen yawon shakatawa. Na kan yi tunanin duk yawan al’ummar kasar Sin da fadin kasar, gwamnati ba ta manta da su ba. Yayin wata ziyarata a lardin Gansu shekaru 5 da suka wuce, na ziyarci wani kauye mai matukar nisa, inda a kan hanyata na yi tunanin ba za a samu abun kirki a kauyen ba. Sai dai sabanin tunanina, na tarar da kauyen na da komai na jin dadin rayuwa kamar dai sauran wuraren da na ziyarta.

Irin ayyukan da jami’an gwamnatin Sin ke yi karkashin jagorancin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya kara bayyana salon demokradiyya da shugabanci irin na kasar Sin, watau demokradiyya da ake yi domin al’umma mai hidimtawa al’umma, irin wadda ya kamata a ce kasashe masu tasowa suna koyi da ita. (Fa’iza Mustapha)

LABARAI MASU NASABA

Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi

Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

Lu
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya

    Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT
Lu
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi
  • Sulaiman
    An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya
  • Sulaiman
    Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin
  • Sulaiman
    Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU

MASU ALAKA

Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi
Daga Birnin Sin

Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi

September 13, 2026
Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin
Daga Birnin Sin

Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

September 13, 2026
Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”

September 13, 2026
Next Post
Kasar Sin Za Ta Samar Da Karin Agajin Gaggawa Na Yuan Miliyan 100 Ga Venezuela

Kasar Sin Za Ta Samar Da Karin Agajin Gaggawa Na Yuan Miliyan 100 Ga Venezuela

LABARAI MASU NASABA

Manchester Derby: City Ta Nunawa United Kwanji A Old Trafford

Manchester Derby: City Ta Nunawa United Kwanji A Old Trafford

September 13, 2026
Ka Kyale Ni Nayi Wa Mutanen Binuwai Aiki – Gwamna Alia Ga Ortom

Ka Kyale Ni Nayi Wa Mutanen Binuwai Aiki – Gwamna Alia Ga Ortom

September 13, 2026
Ka Kyale Ni Nayi Wa Mutanen Binuwai Aiki – Gwamna Alia Ga Ortom

Makiyaya Sun Yi Asarar Shanu 200,000 Ta Dalilin Rikice-Rikice – MACBAN

September 13, 2026
Lu

Farashin Man Fetur Ya Sake Tashi A Abuja

September 13, 2026
Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi

Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi

September 13, 2026
Lu

Malamai Da Limamai 3,000 Sun Yi Addu’ar Zaman Lafiya Da Nasarar Tinubu A 2027

September 13, 2026
An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya

An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya

September 13, 2026
Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

September 13, 2026
Lu

An Gudanar Da Sallar Zana’idar Tsohon Gwamnan Gongola

September 13, 2026
Yajin Aikin ASUU: Malaman Jami’ar Jihar Kaduna Sun Bijirewa El-rufa’i

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU

September 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.