Jakadan kasar Sin a Saliyo Zhao Yong, ya ce a shekarar 2025 da ta gabata, darajar hada-hadar cinikayya tsakanin Sin da Saliyo ta kai dalar Amurka biliyan 2.3, adadin da ya karu da kusan kaso 30 bisa dari kan na shekarar 2024.
Jakada Zhao Yong, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a ofishin jakadancin Sin dake birnin Freetown, fadar mulkin kasar, yana mai cewa, Saliyo ta fitar da karin kaso 40 bisa dari, na hajojinta zuwa Sin a shekarar ta bara, a gabar da mizanin cinikayyar sassan biyu ya karu da kusan kaso 38 bisa dari, a rabin farko na shekarar nan ta 2026.
Jakada Zhao, ya alakanta wannan ci gaba da manufar nan ta kasar Sin ta kawar da daukacin harajin fito kan hajojin kasar dake shiga kasar Sin, yana mai cewa, yanzu haka ma ana ci gaba da tattaunawa, game da fadada fitar da karin hajojin kasar zuwa Sin, ciki har da man-ja, da Kofi da kuma Koko.
Zhao, ya ce cikin sama da shekaru 55, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Saliyo, sassan biyu na ci gaba da martaba juna da goyon bayan juna, yayin da alakarsu ke kara karfi, kana hadin gwiwarsu na kawance ke kara haifar da tarin alfanu.
Daga nan sai ya bayyana cewa, sama da ‘yan Saliyo 6,000 sun ziyarci kasar Sin a shekarar 2025, wanda hakan ya nuna muhimmin ci gaba, kuma ana daukar karin matakai na saukaka zirga-zirga, da matakan neman biza, da biyan kudaden hidimomi ga masu ziyarar Sin daga kasar. (Saminu Alhassan)













