ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 22, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

EFCC Ta Kafa Tawagar Binciken Atiku, Malami Da Wasu Kan Batun Wutar Mambilla

by Abubakar Sulaiman
11 hours ago

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa (EFCC) ta kafa wata tawaga ta musamman domin binciken wasu ’yan siyasa da tsofaffin jami’an gwamnati da aka ambata a hukuncin kotun sasantawa ta Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya (ICC) kan rikicin aikin samar da wutar lantarki na Mambilla da ke Jihar Taraba.

Majiyoyin Premium Times sun ce shugaban EFCC, Olanipekun Olukoyede, ne ke kula da aikin tawagar.

Matakin ya biyo bayan hukuncin da kotun sasantawa ta ICC da ke Paris ta yanke ranar Alhamis, inda ta yi watsi da wasu buƙatun kamfanin Sunrise Power and Transmission Company Ltd kan Gwamnatin Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Kamfanin, ƙarƙashin Leno Adesanya, ya nemi a biya shi dala miliyan 680 da kuma wasu kuɗaɗen da suka shafi wata taƙaddama da ta kai sama da dala biliyan 2.7. Kotun ta kuma umarci Sunrise da Adesanya su mayar wa Nijeriya kuɗin shari’a da suka kai dala miliyan 11.8.

Daga cikin mutanen da aka ambata a cikin hukuncin akwai tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar; da tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami; da tsohon Ministan Wutar Lantarki da Karafa, Olu Agunloye; da tsohon Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Sambo Dasuki; da ɗansa Abubakar Dasuki; da Abdullahi Yola da Dere Awosika.

LABARAI MASU NASABA

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyu, Sun Kwashe Dabbobi A Sokoto

Gwamnatin Zamfara Ta Ƙara Albashin Ma’aikatan Lafiya Da Kashi 95

Hukumar EFCC na son bincikar wasu mu’amaloli da aka ambata a cikin shari’ar da kuma dangantakarsu da aikin Mambilla.

Game da Atiku, hukuncin ya ambaci biyan dala 500,000 da Leno Adesanya ya yi wa Jennifer Douglas Abubakar, tsohuwar matar Atiku, a shekarar 2003.

Adesanya ya bayyana cewa kuɗin na da alaƙa da wata mu’amalar canjin kuɗi da aka yi wa Atiku, amma kotun ta ce ba a gabatar da isassun takardun da za su tabbatar da wannan bayani ba. Sai dai kotun ba ta ce Atiku ya karɓi cin hanci ko ya yi amfani da matsayinsa wajen bai wa Sunrise kwangilar Mambilla ba.

A nasa martanin, Atiku ya musanta cewa kotun ta tuhume shi ko ta same shi da laifi, yana mai cewa ba shi ne ya bayar da kwangilar aikin ba.

Mai magana da yawunsa, Phrank Shaibu, ya kuma ƙalubalanci masu sukar Atiku da su nuna inda hukuncin ya ce ya karɓi cin hanci ko ya shiga wata makarƙashiyar cin hanci. Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da cewa yana sane da batun kafa tawagar, amma ya ce ba a yi masa cikakken bayani kan aikin tawagar ba.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Ceto Mutane 23 Da Aka Yi Garkuwa Da Su, Sun Kama Mutum 4 A Sakkwato
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Biya Ƴan Fansho Naira Biliyan 1.1
  • Abubakar Sulaiman
    Zargin Taimakwa Ƴan Bindiga, Mai PoS Ya Shiga Hannu A Katsina
  • Abubakar Sulaiman
    Dole Tinubu Yayi Bayin Dalilin Rashin Halartar UNGA Har Sau 3 – Atiku

MASU ALAKA

Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
Labarai

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyu, Sun Kwashe Dabbobi A Sokoto

September 21, 2026
Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York
Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Ƙara Albashin Ma’aikatan Lafiya Da Kashi 95

September 21, 2026
Saudiyya Ta Bai Wa NAHCON Shekaru Uku Ta Koma Tsarin Aikin Hajji Na Zamani 
Manyan Labarai

Saudiyya Ta Bai Wa NAHCON Shekaru Uku Ta Koma Tsarin Aikin Hajji Na Zamani 

September 21, 2026
Next Post
Darajar Hatsin Da Za A Noma A Kasar Sin Za Ta Zarce Yuan Tiriliyan 4.5 A Tsakanin 2026 Zuwa 2030

Darajar Hatsin Da Za A Noma A Kasar Sin Za Ta Zarce Yuan Tiriliyan 4.5 A Tsakanin 2026 Zuwa 2030

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York

An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York

September 21, 2026
Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu

Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu

September 21, 2026
Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya

Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya

September 21, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyu, Sun Kwashe Dabbobi A Sokoto

September 21, 2026
Ko Wadanne Gudanmawa Manufar Gaggauta Cinikayyar Waje Ta Sin A Fannin Hajojin Dakile Sauyin Yanayi Ka Iya Samarwa Duniya?

Ko Wadanne Gudanmawa Manufar Gaggauta Cinikayyar Waje Ta Sin A Fannin Hajojin Dakile Sauyin Yanayi Ka Iya Samarwa Duniya?

September 21, 2026
Xi Ya Mayar Da Amsar Wasikar Daliban Jami’o’in Amurka

Xi Ya Mayar Da Amsar Wasikar Daliban Jami’o’in Amurka

September 21, 2026
Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York

Gwamnatin Zamfara Ta Ƙara Albashin Ma’aikatan Lafiya Da Kashi 95

September 21, 2026
Xi Zai Je Ziyarar Aiki A Amurka Daga Ranar 23 Zuwa 25 Ga Watan Satumba

Xi Zai Je Ziyarar Aiki A Amurka Daga Ranar 23 Zuwa 25 Ga Watan Satumba

September 21, 2026
Saudiyya Ta Bai Wa NAHCON Shekaru Uku Ta Koma Tsarin Aikin Hajji Na Zamani 

Saudiyya Ta Bai Wa NAHCON Shekaru Uku Ta Koma Tsarin Aikin Hajji Na Zamani 

September 21, 2026
Sin Ta Yi Nasarar Noma Nau’o’in Tsirrai 14 A Cibiyarta Ta Binciken Sararin Samaniya

Sin Ta Yi Nasarar Noma Nau’o’in Tsirrai 14 A Cibiyarta Ta Binciken Sararin Samaniya

September 21, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.