ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

EFCC Ta Sake Buɗe Binciken Zarge-Zargen Cin Hanci Kan Atiku

by Muhammad
1 week ago

Hukumar EFCC ta sake buɗe binciken zarge-zargen laifukan kuɗi da ake dangantawa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, bayan wani tsohon ɗan majalisar wakilai ya shigar da ƙara yana neman a gurfanar da shi a gaban kotu.

Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta sake buɗe binciken zarge-zargen da ake yi wa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, bayan wani tsohon ɗan majalisar wakilai, Hon. Ehiozuwa Johnson Agbonayinma, ya shigar da ƙara yana neman a ɗauki matakin shari’a kan lamarin.

Ƙarar ta buƙaci hukumar da ta sake duba wani bincike da ya samo asali tun shekarar 2006, lokacin da Mallam Nuhu Ribadu ke shugabantar EFCC, tare da yin nazari kan wani rahoto da wani ƙaramin kwamiti na Majalisar Dattawan Amurka ya fitar daga baya.

ADVERTISEMENT

Da yake magana kan matakin, Agbonayinma ya ce EFCC ta tabbatar masa da cewa ta karɓi ƙarar da ya shigar a ranar 27 ga Agusta, 2026, wadda aka miƙa wa hukumar a ranar 1 ga Satumba, 2026.

An shigar da ƙarar ne ta hannun lauyansa, Chief Hannibal Egbe Uwaifo, SAN, inda aka buƙaci hukumar ta sake buɗe binciken da ta gudanar a baya tare da ɗaukar matakan da suka dace kan zarge-zargen.

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Tsohon ɗan majalisar ya kuma je hedikwatar EFCC da ke Jabi, Abuja, inda ya tabbatar da ƙarar tasa tare da amsa tambayoyin masu binciken hukumar.

Agbonayinma ya ce bai kamata a bar batun ya ci gaba da zama ba tare da an warware shi ba.

Ya ce, “Ina so in gode wa ’yan Nijeriya, EFCC da kuma waɗanda ke yi mini addu’a a wannan fafutuka. Dokokin ƙasa na kowa ne, masu kuɗi da talakawa. Bayan EFCC ta yi kyakkyawan aiki, bai kamata a ɓoye shi a ƙarƙashin tebur ba.”

A cikin ƙarar, Agbonayinma ya buƙaci EFCC ta sake duba rahoton da ta fitar a watan Satumba na shekarar 2006 kan Atiku, da kuma rahoton da ƙaramin kwamitin binciken harkokin kuɗi na Majalisar Dattawan Amurka ya fitar a ranar 4 ga Fabrairu, 2010.

Ya yi iƙirarin cewa waɗannan rahotanni ya kamata su zama ginshiƙin sake ɗaukar mataki kan batun.

Ƙarar ta kuma yi zargin cewa a baya EFCC ta nuna cewa Atiku zai iya fuskantar tuhuma bayan ya bar muƙaminsa na mataimakin shugaban ƙasa, lokacin da kariyar shari’ar da kundin tsarin mulki ya tanadar masa saboda muƙaminsa za ta ƙare.

Sai dai, a cewar Agbonayinma, ba a gurfanar da shi a gaban kotu ba bayan barin muƙamin.

Tsohon ɗan majalisar ya bayyana abin da ya kira rashin ɗaukar mataki a matsayin sakaci wajen gudanar da aiki, yana mai cewa bin diddigin lamarin zai nuna ƙudirin hukumar na tabbatar da cewa manyan mutane masu tasiri a siyasa ma suna fuskantar bincike idan ana zargin sun aikata laifi.

Ya kuma bayyana cewa ya shigar da ƙara ga Shugaban Amurka, Donald Trump, kan zarge-zargen.

A halin da ake ciki, mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, bai mayar da martani kan saƙonnin da aka aika masa domin neman ƙarin bayani game da halin da binciken yake ciki ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    2027: Matawalle Ya Bai Wa ’Yan Majalisar Zamfara Takwas Motocin Alfarma Kirar SUV
  • Muhammad
    UTME: Ɗalibai 108 Daga 39,000 ’Yan Ƙasa Da Shekaru 16 Ne Suka Cika Sharuddan Shiga Jami’a
  • Muhammad
    ’Yan Sanda Sun Kama ’Yan Ƙungiyoyin Asiri Takwas da Masu Damfarar ATM Uku A Kogi
  • Muhammad
    Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Ɗan Majalisa Na Watanni 3 Kan Fitar Bidiyon Jan Kunnen Zomo

MASU ALAKA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu
Manyan Labarai

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau
Manyan Labarai

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Next Post
Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Canton Fair Karo Na 140

Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Canton Fair Karo Na 140

LABARAI MASU NASABA

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026
NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.