Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana faɗaɗa jerin sunayen mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC a matsayin wani “furucin nuna fargaba a sarari”, yana mai zargin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da fifita haɗakar ƴan siyasa a kan matsanancin halin ƙuncin rayuwa da rashin tsaron da ke addabar ƴan ƙasa.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Laraba, Atiku ya bayyana cewa cusa ɗaruruwan sunayen jiga-jigan siyasa a cikin kwamitin kamfe ba zai taɓa magance yunwa ko goge gazawar gwamnatin APC ba. Ya jaddada cewa mutumin da ke tsoron tarihin ayyukansa ne kawai zai yi tunanin zai iya binne gazawarsa a ƙarƙashin tarin sunayen gwamnoni, da ministoci, da ƴan canjin sheƙa, alhali mutane na jiran mafita ne ba sabon jerin sunayen masu kamfe ba.
Atiku ya kuma yi tir da matakin rantsar da kwamitin yaƙin neman zaɓen na jam’iyya mai mulki a Zauren Taron Gidan Gwamnatin Tarayya (Banquet Hall, Presidential Villa) da ke Abuja, inda ya bayyana amfani da kadarorin gwamnati domin buƙatun jam’iyya a matsayin zallar cin zarafin ofishin shugaban ƙasa da dukiyar al’umma.
Jam’iyyar APC dai ta fara fitar da jerin sunayen kwamitin nata ne a ranar 22 ga watan Agusta inda ta naɗa tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin Babban Daraktan Kamfen, kafin daga bisani ta faɗaɗa jerin domin haɗa wa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da sauran ƴan siyasa. Sai dai Atiku ya ce jam’iyyar ADC ta kafa ƙaramin kwamiti mai tsari da zai mayar da hankali kan matsalolin da suka shafi tsadar rayuwa da tsadar makaranta.
A ƙarshe, Atiku ya gargaɗi Shugaba Tinubu cewa a ranar kaɗa ƙuri’a babu wani ginshiƙi a takardar zaɓe da za a auna girman kwamitin kamfen da ɗan takara ya kafa. Ya jaddada cewa ƴan Nijeriya za su yi hukunci ne bisa halin matsi da suka fuskanta a ƙarƙashin gwamnatinsa, kuma a ranar zaɓe zai fuskanci ƴan ƙasar da suka sha wuyar manufofinsa waɗanda adadinsu ya ninka na kowane kwamiti.














