ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kyawawan Manufofin Buhari Za Su Ci Gaba Da Yi Wa ’Yan Nijeriya Tasiri – Tinubu

by Sadiq
2 months ago

Shugaba Bola Tinubu, ya ce kyawawan manufofi da abubuwan da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya bari za su ci gaba da zaburar da ’yan Nijeriya na tsawon shekaru masu zuwa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja yayin taron addu’ar cika shekara ɗaya da rasuwar Buhari.

Mataimakinsa, Kashim Shettima ne, ya wakilce shi a wajen taron.

ADVERTISEMENT

Shugaban ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai kishin ƙasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa Nijeriya hidima da kuma taimakawa wajen ci gaban ƙasar.

Ya ce za a ci gaba da tunawa da Buhari saboda gaskiya, ladabi da jajircewarsa wajen yi wa jama’a hidima.

LABARAI MASU NASABA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

Tinubu ya ce har yanzu ’yan Nijeriya da dama na mutunta Buhari duk da cewa ya bar mulki, sannan ya ƙarfafa wa jama’a gwiwa su ci gaba da riƙe ƙa’idoji wajen gudanar da rayuwa.

Ya ce Nijeriya ba za ta manta da Buhari ba saboda irin rayuwar da ya yi da kuma gudummawar da ya bayar wajen ci gaban ƙasar.

Tinubu ya tuna da dangantakarsa ta siyasa da Buhari, inda ya ce sun yi aiki tare bisa manufa ɗaya ta gina Nijeriya mai zaman lafiya, haɗin kai da wadata.

Ya ƙara da cewa Buhari ya yi wa ƙasar hidima da ƙarfinsa da sadaukarwa.

A cewar Tinubu, Buhari na daga cikin ’yan Nijeriya da suka jagoranci ƙasar a matsayin shugaban soji sannan kuma suka zama shugaban ƙasa ta hanyar zaɓen dimokuraɗiyya.

Ya ce tasirin Buhari ya ginu ne a kan gaskiya, ɗabi’a ta gari da hidimar jama’a, ba wai neman yabo ba.

Shugaban ya kuma miƙa ta’aziyya ga iyalan Buhari tare da tabbatar musu cewa gwamnati za ta ci gaba da kasancewa tare da su.

Ya ce ya kamata ’yan Nijeriya su yi riƙo da halayen da Buhari ya yi fice da su, kamar gaskiya da sauƙin kai.

Tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, Janar Yakubu Gowon, shi ma ya karrama Buhari, inda ya bayyana shi a matsayin jarumin soja da ya yi aiki don tabbatar da haɗin kan Nijeriya.

Gowon ya ce nasarar Buhari a siyasa ta ƙara ƙarfi ne bayan ya yi haɗin gwiwa da Tinubu, wanda ya taimaka masa wajen lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2015.

MASU ALAKA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Gurfanar Da Tubabbun ’Yan ta’addan Da Suka Sake Aikata Manyan Laifuka

Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Gurfanar Da Tubabbun ’Yan ta’addan Da Suka Sake Aikata Manyan Laifuka

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

September 11, 2026
Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

September 11, 2026
Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.