Yau Alhamis da rana, firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa garin Gyirong da ke yankin Xizang mai cin gashin kansa na kudu maso yammacin kasar Sin, bayan mummunar zaftarewar laka ta afkawa garin da jiya safiyar Laraba, agogon kasar Sin.
Li, wanda kuma memba ne na zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya tafi wurin ne bisa umarnin Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, don ya jagoranci wata tawagar manyan jami’ai daga mabambantan hukumomi masu ruwa da tsaki, zuwa yankin da bala’in ya shafa.
Wadannan jami’ai za su sanya ido kan ayyukan ceto da agaji, sannan za su ziyarci wurare daban daban don ganawa da ma’aikatan ceto da masu ba da agaji, da kuma mutanen da bala’in ya ritsa da su. (Bello Wang)














