Firaministan kasar Sin, Li Qiang, ya jaddada bukatar ci gaba da karfafa kwazon kasar Sin wajen rigakafin abkuwar ibtla’i, da rage mummunan tasirinsa, da kuma ayyukan agaji domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Li, wanda har ila yau mamba ne a zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya bayyana hakan ne yayin wani rangadin duba ayyuka a birnin Tangshan, da ke lardin Hebei a yankin arewacin kasar Sin.
A wannan shekarar ce aka cika shekaru 50 da abkuwar girgizar kasar Tangshan, girgizar kasar da ta kai karfin maki 7.8 wadda ta abku a birnin ranar 28 ga watan Yulin 1976, inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 240,000 tare da lalata kusan dukkan gine-ginen birnin.
A yayin ziyarar da ya kai wurin tunawa da girgizar kasar ta Tangshan, Li ya ajiye kwandon furanni domin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar da kuma jaruman da suka mutu yayin gudanar da ayyukan ceto da ba da agaji, sannan ya sunkuya sau uku a gaban bangon tunawa da su.
Li ya bayyana cewa, a cikin shekaru hamsin da suka gabata, al’ummar Tangshan sun sake gina birni na zamani daga baraguzan da suka rage bayan abkuwar ibtila’in. Yayin da birnin na Tangshan ke shiga sabon matakin ci gaba.
Kuma ya yi kira ga birnin da ya yi amfani da damammakin da ake samu daga tsarin ci gaba na hadin gwiwa na yankin Beijing-Tianjin-Hebei, tare da cin gajiyar karfinsa na musamman, domin kara inganta yanayin jarumin birnin. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)














