Yanzu dai, karin sabbin abubuwa iri uku kirar Sin masu lakabin “New ‘New Three’’’ wadanda suka kunshi mutum-mutumin inji, da fasahar AI da sabbin magungunan da aka kirkiro, sun mamaye kafafen yada labarai na kasashen waje, har ma su kasance kayayyaki da yanzu Sin ta fi cinikayyarsu da kasashen waje.
Kamfanin dillancin labarai na NBC na Amurka ya rawaito daga sakamakon binciken jin ra’ayoyin jama’a da cibiyar nazari ta Pew ta fitar a ranar 15 ga watan nan cewa, ra’ayin “Sin ita ce amintacciyar abokiyar hadin gwiwa” yana dada samun karbuwa a yankuna da dama na duniya.
A cikin ’yan shekarun nan, Sin ta yi amfani da damar da ke tattare da sauye-sauyen ci gaba ta hanya maras gurbata muhalli, inda karfin samar da kayayyaki da ke karkashin jagorancin motocin fasinja masu amfani da lantarki, da batirin lithium da kuma kayayyakin sola ke samun tasowa kwarai, wandanda ake kira da “New Three”, watau sabbin abubuwa 3 da ake fitarwa zuwa kasashen waje. Yanzu dai, Sin tana himmatuwa sosai wajen inganta kayayyakin New “New Three”, da kuma tabbatar da sauyawar alkiblar masana’antu daga “kirar Sin” kawai zuwa “kirar Sin mai aiki da basira”.
Yayin da wasu kasashen yamma ke gitta shinge da katanga, Sin ta dage da yin kirkire-kirkire a bude, wanda hakan ke kawo wa duniya sabuwar dama ta bude kofa da hadin kai. Karin sabbin abubuwa iri uku kirar Sin da ake kira da “New ‘New Three’’’ wadanda ke jagorantar samar da bunkasa ta nan gaba ta hanyar basira, ba sabon injin bunkasar tattalin arzikin Sin ba ne kawai, har ma muhimmin karfi ne da ke kara azama ga kasashe daban daban wajen samun wadata tare.
Wannan kuma ya sake tabbatar da cewa, ci gaban da kasar Sin ke kawo wa duniya, ba girgiza wasu ba ne, a’a, dama ce, kuma ba barazana ba ce, a’a, hanya ce ta kara karfin ci gaban kasashen duniya. (Bilkisu Xin)














