Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi, ya bukaci rundunar sojin Nijeriya da gwamnati su dauki sabon salo wajen yaki da ’yan bindiga da masu tayar da kayar baya, yana mai cewa dogaro da karfin soja kadai bai kawo karshen matsalar tsaro a wasu sassan kasar ba.
Da yake magana yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kaduna, Gumi ya ce salon amfani da karfin soja da aka yi amfani da shi kan kungiyoyin masu dauke da makamai cikin shekaru 17 da suka gabata bai samar da zaman lafiya mai dorewa ba, musamman tun bayan tsanantar rikicin Boko Haram a shekarar 2009.
Ya ce, “Idan salon amfani da karfin soja bai yi aiki ba tsawon shekaru 17, me ya sa ba za mu sauya salo ba?”
Malamin ya ba da shawarar yin sulhu, gyaran hali da sake mayar da ’yan bindigar da suka tuba cikin al’umma a matsayin wani bangare na kokarin dawo da zaman lafiya a yankunan da matsalar ta shafa.
A cewarsa, yunkurin sulhun da aka taba yi a jihohi kamar Katsina da Zamfara bai yi nasara ba ne saboda hukumomi sun fi mayar da hankali kan biyan kudi ba tare da samar da shirye-shiryen gyaran hali na dogon lokaci ba.















Discussion about this post