Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana matuƙar alhininsa kan rasuwar Sarkin Zamfaran Zurmi, Mai Martaba Alhaji Bello Sulaiman.
Mai martaban ya rasu ne a ranar Litinin a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Talata, Gwamna Lawal ya bayyana rasuwar Sarkin a matsayin babban rashi ga iyalansa, Masarautar Zurmi, harkokin gargajiya da kuma al’ummar Jihar Zamfara baki ɗaya.
Gwamnan ya ce rasuwar Mai Martaba Alhaji Bello Sulaiman ta girgiza shi matuƙa, yana mai cewa za a riƙa tunawa da Sarkin bisa irin hidimar da ya yi wa al’ummarsa, gudunmawar da ya bayar wajen ƙarfafa masarautun gargajiya da kuma ƙoƙarinsa na ganin an samu zaman lafiya da ci gaban Jihar Zamfara.
“Ina matuƙar baƙin ciki da rasuwar Mai Martaba Alhaji Bello Sulaiman, Sarkin Zamfaran Zurmi.
“Rasuwarsa babban rashi ne ga Jihar Zamfara. Za a riƙa tunawa da shi bisa hidimar da ya yi wa al’ummarsa, gudunmawar da ya bayar ga masarautar gargajiya da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jiharmu,” inji Gwamna Lawal.
Ya ƙara da cewa, a madadin Gwamnatin Jihar Zamfara da al’ummar jihar, yana miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, Majalisar Masarautar Zurmi da ɗaukacin al’ummar Masarautar Zurmi.
Gwamnan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya saka masa da alheran da ya aikata, Ya ba shi Aljannar Firdausi, tare da bai wa iyalansa da al’ummar Zurmi haƙurin jure wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba.














