ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Lawal Ya Amince Da Wani Shirin Gaggawa Don Ceto Ilimi A Zamfara

by Sulaiman
5 months ago

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da wani shiri na musamman na kwanaki 120 domin magance manyan matsalolin da ke addabar tsarin ilimi a jihar.

Gwamnan ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar 65 a Gidan Gwamnati da ke Gusau a ranar Litinin, inda aka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi bangarori daban-daban, ciki har da ilimi, lafiya da ayyukan raya ƙasa.

A cewar wata sanarwa, “A zaman Majalisar zartarwar na 65, gwamnatin ta amince da wani tsari na gaggawa da aka gina ne bisa bincike da nazarin da Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Tabbatar da Ingancin Ilimi ta Jihar (EQAA) suka gudanar a baya.”“Shirin na kwanaki 120, wanda muƙaddashin Kwamishinan Ilimi, Abdulmalik Abubakar Gajam ya gabatar, ya ƙunshi matakai da suka haɗa da tantance ma’aikata ta hanyar duba albashi, tsara taswirar makarantu da kuma duba yanayin gine-ginen makarantu.

ADVERTISEMENT

Haka kuma, shirin ya tanadi aiwatar da sauye-sauye cikin gaggawa a bangarorin gudanarwa, gine-gine, fasahar zamani, horas da malamai da kuma kula da jin daɗin ɗalibai, domin tabbatar da ingantaccen tsarin ilimi a jihar.

Bugu da ƙari, Majalisar ta amince da kafa wani kwamiti na haɗin gwiwa ƙarƙashin jagorancin Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha, domin bincike da tantance dukkan gine-ginen da aka gina ba bisa ƙa’ida ba a kusa da makarantu.

LABARAI MASU NASABA

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

An kuma ba kwamitin umarnin ɗaukar matakin kwashe irin waɗannan gine-gine domin tabbatar da tsaro da tsaftar muhallin makarantu.

A wani muhimmin mataki, Majalisar ta amince da samar da dokar haɗaka guda ɗaya da za ta rufe dukkan matakan ilimi daga na yara ƙanana (ECCDE) zuwa manyan makarantu. An bayyana cewa za a gabatar da ƙudirin dokar ga Majalisar Dokokin Jihar domin amincewa da shi cikin gaggawa.

Haka kuma, Gwamna Lawal ya amince da sauya tsarin biyan albashi ga ma’aikatan da ba malamai ba, inda za a mayar da su zuwa wasu ma’aikatun gwamnati ko kuma kamfanoni masu zaman kansu, domin inganta tsarin aiki da rage cunkoso a bangaren ilimi.

Majalisar ta kuma amince da kafa Kwamitin Jagoranci na Jihar kan Dokar Ta-baci a Fannin Ilimi, tare da bai wa kwamitin damar kafa Kwamitin Kwararru (Technical Working Group) da kuma haɗa gwiwa da masu ruwa da tsaki kamar Ƙungiyar Malamai (NUT), UNICEF, Hukumar Ilimin Firamare ta Tarayya (UBEC), shugabannin gargajiya da na addini, masu makarantu masu zaman kansu da ƙungiyoyin farar hula.

Wannan mataki na nuna ƙudirin gwamnatin Zamfara na farfaɗo da bangaren ilimi, tare da tabbatar da cewa an magance matsalolin da suka daɗe suna tarnaƙi ga cigaban ilimi a jihar.

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Labarai

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Next Post
Xi Jinping Ya Gana Da Firaministan Kasar Sifaniya

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.