Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya karɓi lambar yabo ta musamman daga Gwamnatin Tarayya a matsayin jinjina ga irin gagarumar rawar da yake takawa wajen bunƙasa tattalin arziƙi da ƙarfafa wa mata gwiwa (WEE) a jiharsa, musamman ta hanyar aniyarsa kan shirin tallafa wa mata na Nijeriya (NFWP).
An bayar da wannan lambar yabon ne a yayin taron Majalisar Ƙasa kan Harkokin Mata, Ci gaban Yara, da Walwalar Al’umma karo na 26 wanda aka gudanar a garin Jalingo na Jihar Taraba a ranar 14 ga watan Agustan 2026.
Kwamishiniyar Harkokin Mata ta jihar, Honarabul Aisha Aminu Malumfashi, ita ce ta wakilci gwamnan inda ta karɓi lambar yabon a madadinsa. Daga bisani, ta miƙa wannan kyauta ga Gwamna Radda a lokacin taron Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 14 wanda aka gudanar a Gidan Gwamnatin Katsina a jiya.
An gudanar da taron majalisar na ƙasa ne ƙarƙashin taken, “Ƙarfafa Iyalai da Bunƙasa Tattalin Arziƙin Kula da Jama’a don Samun Ci Gaba Mai Haɗa Kowa da Kowa: Aiwatar da Sabon Tsarin Kariya ga Al’umma na Nijeriya.”
A cewar wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a yau 28 ga watan Agusta, wannan yabo ya nuna irin namijin ƙoƙarin da gwamnatin Radda ke yi wajen kyautata rayuwa da bunƙasa tattalin arziƙin mata a fadin Jihar Katsina.
Ya bayyana cewa hakan na nuni da ƙoƙarin da gwamnatin ke ci gaba da yi na faɗaɗa damar mata wajen samun kuɗaɗen jarin kasuwanci da kuma koyon sana’o’in hannu domin su zama masu dogaro da kai.
Sanarwar ta ƙara da cewa ta hanyar waɗannan tsare-tsare, gwamnatin na ci gaba da inganta hanyoyin samun kuɗin shiga ga iyalai daban-daban, tare da samar da ɗorewar tattalin arziƙi ga mata domin su bayar da gudunmawa mai tsoka wajen ci gaban jihar.
Har ila yau, lambar yabon ta sake fito da aniyar Gwamna Radda na mayar da shirin karfafawa mata a matsayin wani muhimmin ginshiƙi na ci gaban al’umma da kuma gina Jihar Katsina mai ƙarfin arziƙi da juriya.













