Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da kafa kwamitin Jiha kan rarraba takin zamani, a cikin ƙoƙarinsa na tabbatar da an yi rabon kayan aikin noma ga manoma a lokacin daminar bana ta shekarar 2026 yadda ya kamata.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, wanda ya sanar da amincewar Gwamnan, ya bayyana cewa an bai wa kwamitin umurnin sanya ido kan yadda ake rarraba takin zamani yadda ya kamata a faɗin jihar, tare da tabbatar da cewa takin ya isa hannun manoma na gaskiya a dukkan sassan Jihar Gombe, domin ƙara bunƙasa noman amfanin gona da ƙarfafa samar da isasshen abinci.
An nada Kwamishinan ma’aikatar noma da tsaron abinci na jihar a matsayin shugaban kwamitin, yayin da babban sakataren ma’aikatar ƙananan hukumomi, mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin noma, shugaban kwamitin majalisar dokokin Jihar kan harƙoƙin Noma, da Daraktan Noma na Ma’aikatar Noma na Jiha za su kasance mambobin kwamitin.
Wakilan ƙungiyoyin fararen hula (CSOs) a cikin kwamitin su ne Ibrahim Yusuf 3000, Farfesa Tahir Inuwa da Rabaran Chris Godobe.Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da wakilan ƙungiyar Manoma ta Nijeriya (AFAN), reshen Jihar Gombe; rundunar Ƴansandan Nijeriya; gyaran hali, jami’i daga DSS; wakili daga hukumar Tsaron fararen hula ta Nijeriya (NSCDC); da kuma wakilin masu buƙata ta musamman.
A cewar SSG, babban Sakataren Ma’aikatar Noma shi ne zai kasance Sakataren kwamitin.














