An fara taron jami’an kula da yankunan karkarar Afrika kan dabarun yaki da talauci, jiya Alhamis a birnin Xining na lardin Qinghai na kasar Sin. Taron wanda shi ne irinsa na farko, ya samu halartar jami’ai 33 masu ruwa da tsaki a harkokin kula da yankunan karkara da matasa ’yan kasuwa da wakilan kungiyoyi masu zaman kansu, daga kasashen Afrika 9 da suka hada da Angola da Congo (Brazzaville) da Guinea da Ghana da Kenya da Liberia da Afrika ta Kudu da Nijeria da kuma Tanzania.
A bana ake cika shekaru 70 da fara kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da kasashen Afrika, kuma an ayyana bana a matsayin shekarar musayar al’adu tsakanin Sin da Afrika. Taron na bayar da horo na tsawon kwanki 6, na mayar da hankali ne kan batutuwa kamar na rage talauci da neman ci gaba da inganta rayuwar jama’a da harkokin shugabancin yankunan karkara.
Lardin Qinghai ya tsara wasu jerin matakan da za a iya kwaikwaya a bangarori kamar na zamanantar da aikin gona da samun riba daga ayyukan kare muhalli da kirkiro sabbin dabaru a harkar shugabancin kauyuka, wadanda za su zama abun koyi ga kasashen Afrika a fagen yaki da talauci. (Fa’iza Mustapha)














