Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya taya Sanata Rabiu Kwankwaso murnar cika shekaru 70 a duniya.
Wannan n cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Sunusi Bature, ya fitar a ranar Talata.
Yusuf ya yaba wa Kwankwaso bisa gudummawar da ya bayar wajen ci gaban Kano da Nijeriya.
Gwamnan ya bayyana ranar haihuwar Kwankwaso a matsayin wata dama ta karrama jagorancinsa da hidimar da ya yi wa al’umma, musamman a fannin siyasa, samar da ababen more rayuwa da bunƙasa dimokuraɗiyya a Kano.
Yusuf ya yi addu’ar Allah Ya ba Kwankwaso lafiya, tsawon rai domin ya ci gaba da bayar da gudummawa ga ci gaban Jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.














