ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

’Yansanda Sun Ceto Yaro Mai Shekara Shida Da Aka Sace, Sun Cafke Wanda Ake Zargi A Borno

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago
'Yansanda

Rundunar ’Yansandan Jihar Borno ta yi nasarar ceto wani yaro mai shekaru shida da aka yi garkuwa da shi a Maiduguri, tare da kama wani mutum da ake zargi da hannu a aikata laifin.

Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakinta, Nahum Daso, ya fitar a ranar Litinin.

A cewar Daso, yaron mai suna Alkali Musa, mazaunin unguwar Mafoni da ke Maiduguri, ya bace ne bayan ya fita wasa a ranar 6 ga Yuni amma bai dawo gida ba.

ADVERTISEMENT

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ya ce binciken farko ya nuna cewa jim kadan bayan batan yaron, wanda ake zargin ya tuntubi iyayensa tare da neman kudin fansa na Naira 200,000 kafin a sake shi.

Ya bayyana cewa bayan samun rahoton lamarin a ranar Lahadi, DPO na ofishin ’yansanda na Lamisula ya tattara tawagar jami’an bincike tare da kaddamar da wani aiki na musamman na tattara bayanan sirri domin gano wanda ake zargin da kuma ceto yaron.

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

Sanarwar ta ce: “A ranar 7 ga Yuni, 2026, da misalin karfe 2:00 na rana, rundunar ta samu rahoton batan wani yaro mai suna Alkali Musa, dan shekara shida daga yankin Mafoni a Maiduguri, wanda ya fita wasa a ranar 6 ga Yuni, 2026 amma bai dawo gida ba.

“Binciken farko ya nuna cewa jim kadan bayan batan yaron, wanda ake zargin ya tuntubi iyayensa tare da neman kudin fansa har Naira 200,000 domin a sake shi.”

Daso ya ce wannan aiki ya kai ga cafke wanda ake zargin, mai suna Ali Alhaji Ali, tare da ceto yaron cikin koshin lafiya.

Sanarwar ta kara da cewa an ceto yaron ba tare da ya ji rauni ba, sannan an hada shi da iyalansa.

“Kokarin da aka yi ya samar da sakamako mai kyau, inda aka kama wanda ake zargin, Ali Alhaji Ali, tare da ceto yaron ba tare da wani rauni ba.

“Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, kuma an mika shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin ci gaba da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da shi a kotu,” in ji sanarwar.

Da yake mayar da martani, Kwamishinan ’Yansandan Jihar Borno, Naziru Abdulmajid, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa saurin martani da kwarewar da suka nuna.

Ya kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.

“Kwamishinan ’Yansanda na Jihar Borno, Naziru Abdulmajid, ya yaba da saurin matakin da jami’an suka dauka a wannan aiki, tare da tabbatar wa jama’a cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.

“Haka kuma rundunar tana kira ga iyaye da masu kula da yara da su kasance masu sa ido sosai kan ‘ya’yansu, tare da karfafa wa jama’a su rika kai rahoton duk wani mutum ko motsi da suke zargi ga ofishin ’yansanda mafi kusa,” in ji sanarwar.

A wani labari makamancin wannan, an ruwaito cewa a ranar 25 ga Afrilu, Rundunar ’Yansandan Jihar Kano ta ceto wani yaro dan shekara biyu da aka sace, tare da kama mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin, sannan ta kwato Naira 930,000 daga cikin kudin fansar da iyalan yaron suka biya.

Kakakin rundunar a Kano, Abdullahi Kiyawa, ya bayyana cewa an yi garkuwa da yaron ne kafin daga bisani jami’an tsaro su ceto shi ta hanyar wani aiki na musamman da ya dogara da bayanan sirri.

'Yansanda
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Amfani Da Tsaron Kasa Wajen Danne Wasu Kamfanonin Sinawa

Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Amfani Da Tsaron Kasa Wajen Danne Wasu Kamfanonin Sinawa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.