ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello

by Leadership Hausa
2 months ago
Zamani

Malama Ramatu Bello Hamza, matashiya ce da yi fice a tsakanin tsararrakinta domin kuwa ta rungumi lamarin zaman gidan miji da karatun boko da kuma sana’a, ba ta bari wani ɓangare ya cutar da wani ɓangare ba. A tattaunawar da wakilinmu Muhammad Baƙir Bello ta bayyana yadda ta fuskanci karatun boko har zuwa matakin MASTERS da kuma yadda take ribatar kafafen sadarwa na zamani wajen bunƙasa kasuwanci ta. Ga dai yadda hirar ta kasance

Masu karatu za su so jin taƙaitatcen tarihinki

Sunana Ramatu Bello Hamza, an haifeni a garin Samaru Zaria. Na yi karatun Firamari da Sakandare duk a nan garin Samaru. Na yi difloma, degree da masters ɗina a nan Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Na kuma yi karatun difloma a ɓangaren Kwanfuta, haka kuma na sauke tilawar Alku’ani mai Tsarki na kuma yi karatun litattafan addini daidai gargwado.

ADVERTISEMENT

Ta yaya kika tsinci kanki a wannan harkar sana’a ta kafafen sadarwa na zamani (sohiyal midiya)?

Na fara shiga harkar yanar gizo ne domin faɗaɗa kasuwancina da kuma samun damar isa ga kwastomomi masu yawa, a halin yanzu zamani ya zo da wannan ci gaba kusan kowa yana amfani da wayar hannu kuma yana hulɗa da kafafen sadarwa (Soshiyal Midiya), saboda haka yana sauƙin gaske mutum ya sadu da mutane da dama a cikin lokaci kaɗan ta wannan hanyar. Na fara tallata hajojina kamar kayan kitchen, kayan sawa, da kuma ADASHEN GATA ta hanyar kafafen sada zumunta. Da jajircewa, gaskiya da kyakkyawar mu’amala da kwastomomi, harkar ya ci gaba da bunƙasa, har na samu amincewa daga mutane da dama.

LABARAI MASU NASABA

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa

Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

Zamani

Zuwa yanzu kin yi shekara nawa kina wannan Sana’ar?

Zuwa yanzu na yi shekara 5 ina wannan sana’ar

Yaya tsarin ADASHEN GATA yake?

Tsari ne da yake ba mutum damar mallakar kayan da yake buƙata ta hanyar biyan kuɗaɗen kayan a hankali ta hanyar zuba kuɗi a hankali har ya kammala sannan ya kwashi kayansa. Daga farawa zuwa yanzu al’umma da dama sun amfana kuma ana kuma ta godiya. Sirrin da ke tattare da haka kuma shi ne gaskiya da riƙon amana musamman a wannan lokacin da ƴan damfara suka cika kafafen sadarwa.

Ta yaya kika iya hada karatu da Sana’a?

Na iya haɗa karatu da sana’a ne ta hanyar tsara lokacina yadda ya kamata. Ina ba karatu fifiko a lokutan karatu, sannan ina gudanar da sana’ata a lokacin da nake da hutu ko bayan na kammala abin da ya shafi karatu. Haka kuma, ina amfani da wayata da kafafen yanar gizo wajen karɓar oda da kula da kwastomomi ba tare da hakan ya kawo cikas ga karatuna ba. Ina ganin idan mutum yana da tsari, jajircewa, da haƙuri, zai iya haɗa karatu da sana’a cikin nasara.

Wasu irin ƙalubane kika fukanta?

Na fuskanci ƙalubale da dama a farkon fa ra sana’ata. Daga ciki akwai ƙarancin jari, samun kwastomomi, da kuma haɗa lokaci tsakanin karatu da sana’a. Wani lokaci kuma ina fuskantar jinkirin biyan kuɗi daga wasu kwastomomi ko rashin fahimtar muhimmancin sana’ar daga wasu mutane. Amma ban yi ƙasa a gwiwa ba. Da haƙuri, addu’a, jajircewa, da kyakkyawar mu’amala da kwastomomi, na ci gaba da shawo kan waɗannan ƙalubale. Waɗannan ƙalubalen sun ƙara mini ƙwarewa da ƙarfin guiwa.

Su wa suka zama abin koyi gare ki a fafutkar ki?

Tabbas na samu goyon baya da ƙarfafawa daga iyaye na da sauran al’umma, mahaifina ya tsayu wajen ganin babu wani mataki na karatun boko da ya kubce mini na kuma samu tarbiyar kasuwanci daga mahaifiyata wadda ta koya min yadda zan juya kwabo da taro da sisi sai kuma ƴan uwana domin da su nike fara gwajin duk wani abin da zan fara aiwatarwa. Haka kuma maigidana (Mijina) ya matuƙar dafa mini ta hanyar kasancewa tare da ni a duk rintsin dana samu kai na. ina matuwar godiya a garesu.

Wani irin buri kike da shi a wannan Sana’a?

Burina a wannan sana’a shi ne in gina kasuwanci mai ƙarfi da amana, wanda zai zama abin koyi ga sauran mata da matasa. Ina son in faɗaɗa sana’ata har ta kai matakin da zan riƙa samar da ayyukan yi ga wasu, tare da taimaka wa mata su dogara da kansu ta hanyar horo da ƙarfafa su domin fara sana’a. Haka kuma, ina fatan kasuwancina ya bunƙasa har ya zama sananne a faɗin Nijeriya da ma ƙasashen waje. Mafi muhimmanci, ina roƙon Allah Ya sanya albarka a cikinsa, Ya sa ya zama sanadin alheri a gare ni da al’umma baki ɗaya.

Kina da sako na musamman da kike son isar masu karatu?

Sakona ga masu karatu shi ne su ɗauki ilimi da muhimmanci, domin shi ne ginshiƙin ci gaba. Kada su ji tsoron fara sana’a tun suna karatu, muddin za su tsara lokacinsu yadda ya kamata. Su kasance masu haƙuri, jajircewa, da gaskiya a duk abin da suke yi, domin nasara ba ta zuwa cikin dare ɗaya. Kada su raina ƙaramar farawa, domin manyan nasarori da yawa daga ƙananan matakai suke farawa. Haka kuma, su dogara ga Allah, su yawaita addu’a, kuma su kasance masu kyakkyawar ɗabi’a da amana, domin waɗannan sune ginshiƙan samun ɗaukaka da nasara.

Mun gode ƙwarai da gaske

Nima na gode

Zamani
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya

MASU ALAKA

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
Tattaunawa

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa

August 28, 2026
Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina
Tattaunawa

Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

August 20, 2026
Nijeriya
Tattaunawa

2027: Shugaba Mai Gaskiya Da Hangen Nesa Nijeriya Ke Buƙata —Ahmad Shu’aibu

August 8, 2026
Next Post
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.