Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen Naira biliyan 3.5 domin biyan kuɗin ajiya na aikin Hajjin shekarar 2027 ga maniyyata daga jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Sagir Musa, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon taron Majalisar Zartarwa da aka gudanar ranar Talata a Fadar Gwamnati da ke Dutse, babban birnin jihar.
A cewar kwamishinan, amincewar ta nuna ƙudurin Gwamna Umar Namadi na ci gaba da kula da walwalar al’ummar jihar da kuma cika alƙawuran da gwamnatin ta dauka.
ADVERTISEMENT














