ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Kano Ta Rufe Wasu Makarantu 9 Kan Saɓa Doka

by Abubakar Sulaiman
2 weeks ago

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da rufe wasu makarantu masu zaman kansu guda tara (9) a faɗin jihar, biyo bayan samunsu da laifin saɓa ƙa’idojin aiki da rashin cika sharuɗɗan rajista da sabunta lasisin gudanarwa kamar yadda dokokin ilimi na jihar suka tanada.

Matakin ya biyo bayan wani aikin sintiri da tantance ingancin makarantu da Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta Jihar Kano (Kano State Private and Voluntary Institutions Board) ta gudanar tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Ilimi ta jihar a birnin Kano da kewayensa.

Babban Sakataren Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta Jihar Kano (KSPVIB), Kwamared Baba Abubakar Umar, shi ne ya yi jawabi a madadin gwamnatin jihar a yayin wata ganawa da manema labarai (media parley) a birnin Kano.

ADVERTISEMENT

Bayanai sun nuna cewa an ɗauki wannan mataki ne bayan da makarantun suka gaza cika sharuɗɗan da doka ta gindaya, waɗanda suka haɗa da:

Yin aiki ba tare da cikakkiyar rajista a hukumance ba.

LABARAI MASU NASABA

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Rashin sabunta lasisin gudanar da makaranta duk da gargaɗin da aka sha yi musu a baya.

Gudanar da koyo da koyarwa a wuraren da ba su dace da tarbiyya da lafiyar ɗalibai ba.

Rashin isassun kayan aiki da ƙwararrun malamai da suka dace da tsarin manhajar karatu.

Hukumar ta jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta lamunci duk wata makaranta da ke gudanar da aiki a ɓoye ko ba bisa ƙa’ida ba, domin hakan na tauye daraja da ingancin ilimin da ake son bai wa al’umma tare da jefa makomar yara cikin ruɗani.

Haka kuma, an gargaɗi sauran masu makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar da su hanzarta zuwa ofishin hukumar domin cika dukkan sharuɗɗan rajista da sabunta lasisansu, tare da ankarar da su cewa aikin rufe makarantu marasa inganci da ba sa bin doka zai ci gaba ba tare da sassautawa ba.

A ƙarshe, hukumar ta yi kira ga iyaye da su riƙa tantance sahihancin makarantun da suke saka ƴaƴansu kafin biyan kuɗin makaranta, domin tabbatar da cewa ɗaliban na karatu ne a wuraren da dokar gwamnatin jiha ta amince da su.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh
  • Abubakar Sulaiman
    Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC
  • Abubakar Sulaiman
    Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’
  • Abubakar Sulaiman
    Aikin Titin Jirgin Ƙasa Na Kaduna Zuwa Kano Ya Kai Kashi 90%

MASU ALAKA

Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35
Manyan Labarai

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu
Manyan Labarai

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
Next Post
Sin Ta Gina Cibiyoyin Luban 38 A Kasashe 32

Sin Ta Gina Cibiyoyin Luban 38 A Kasashe 32

LABARAI MASU NASABA

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

October 23, 2026
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

October 23, 2026
Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

October 23, 2026
Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026
Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

October 23, 2026
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.