ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Shirin Da Gwamnatin Jihar Katsina Ke Yi Wa Manoma Zai  Amfane Su A wannan Daminar?

by Sulaiman and El-Zaharadeen Umar
2 months ago
Katsina

Noma na ɗaya daga cikin manyan sana’o’i ko mu ce ayyuka da mafiyawan al’umma jihar Katsina suka yi dogara da shi a matsayin hanya ta bunƙasa tattalin arziki da samar da cimaka.

To, sai dai, harkar noma ta gamo da babban ciwo wanda har gobe ake neman maganin sa domin a samu a warware ta yadda arziki zai cigaba da wanzuwa a tsakanin al’umma.

Ita ma jihar Katsina ta kasance wani ɓangare da ake tinƙaho da shi, wajen samar da kaso mai yawa a fannin noma shekara da shekaru.

ADVERTISEMENT

Sakamakon wancan cuta da ta kama harkar noma ta sanya hannun agogo ya koma baya, wanda yanzu haka gwamnati ta dukufa ba dare ba rana wajen ganin an dawo da martabar noma ta hanyar yin sa yadda ya kamata.

Tun kafin zuwan damina gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda ta ayyana kudirin ta na bunƙasa harkokin noma ta fannoni daban-daban.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Misalin haka shi ne, mun ga yadda aka fara da manoman rani, inda aka raba masu kayayyakin aikin noma wasu kyauta wasu kuma da kuɗi ƴan ƙalilan domin dai a dawo da martabar noma a jihar Katsina da ta shiga wani hali yau da rai gobe a mace…

A wannan karon an rabawa manoma kayayyakin aikin gona da yawa kuma na zamani da suka haɗa da takin zamani da na’uran huɗa (Power Tllers) ta zamani da kayan samar da ruwa ta hanyar haske rana da irin shuka da sauran su.

Dalilin samar da waɗannan ƙananan taraktoci na zamani shine yadda ɓarayin daji suka raba al’umma da shanun su, ta inda yanzu ganin shanu a wasu yankunan da ke fama da matsalolin tsaro ya zama abin mamaki.

Gwamna Raɗɗa ya ƙara da cewa samar da waɗannan ‘Power Tllers’ zai maye gurbin shanun da aka raba sakamakon hare-haren wuce gona da iri da ƴan bindiga suka riƙa kaiwa suna sace shanun al’umma.

Kazalika an baiwa manoman damina takin zamani akan farashi mai rahusa a ya yin da ake sayar da shi a kasuwa akan naira N50,00 kowane buhu amma ita gwamnati tana sayar da shi akan naira dubu ashirin da biyar.

Sannan ya ɗauki matakai na ganin cewa sai wanda yake manomi kuma ya nuna sha’awar yin noma sannan zai amfana da wannan tallafi na ragin kuɗin taki, kuma ita gwamnati ke ɗaukar nauyin kai duk inda al’umma za su karɓa.

Wannan gagarumin ragi da gwamnatin jihar Katsina ta ɓullo da shi zai taimaka wajen wahalhalun da manoma ke sha kafin samun takin zamani a kowace shekara.

Sannan kamar yadda rahotanni suka bayyana, an samar da wannan taki zamani da wuri sakamakon sauran shekarun baya da sai damina ta yi nisa sannan ake fara rabon takin zamani kuma mai rabo ke samu marar rabo dai kallo

To, sai dai duk wannan shiri da gwamnatin jihar Katsina da tarayya da kuma su kan su manoman da suka yi, ba za a samu nasarar samar da wadataccen abinci ba ta hanyar noma sai idan an samu yin noman yadda aka saba yi a baya sakamakon matsalolin tsaro da suka addabi wasu yankuna karkara.

Wato dai matsalar tsaro da ake fama da ita a wasu yankunan jihar Katsina inda kuma nan ne ginshikin yin noma a jihar har yanzu tana cigaba da maida hannun agogo baya a ƙoƙarin gwamnati na ganin an samu damar yin noma.

Duk lokacin da damina ta sauka ana fama da ƴan bindiga waɗanda suke ƙaƙabawa al’umma haraji idan har suna san yin noma a garuruwan su, sannan babu tabbas idan sun biya kuɗin za a bari su yi noman yadda ya kamata ko kuma su amfana da abinda suka noma.

Abubuwa biyu suke addabar harkokin noma a jihar Katsina, na farko dai tsadar kayan noma da kuma matsalolin ɓarayin daji, to, yanzu gwamnati ta yi huɓɓasa wajen samar da kayayyakin aikin gona ta hanya mai sauki.

Tambayar da kowa ke yi yanzu dai ita ce, wannan shiri da aka yi ko manoma a jihar Katsina za su amfana da ta, domin wancan matsala ta ɓarayin daji tana nan zaune da ƙafafuwanta babu inda ta je, gashi kuma manoma sun yi shiri fiye da kowane lokaci, shin ya a zata kaya ke nan.?

Bayan wancan ƙoƙari na gwamnatin jihar Katsina, ita ma gwamnatin tarayya ta yi na ta huɓɓasa ta inda ta yi gagarumin taron ƙaddamar raba takin zamani na arewa maso yamma a jihar Katsina, kuma wannan taki kyauta ne ba sayarwa ba ake yi na ga manema.

Gwamnatin shugaba Tinubu ƙarƙashin shirin sabinta fata (Renewed Hope) ta hanyar asusun bunƙasa noma na Nijeriya an raba buhun taki 100,800 ga manoma dubu 25,200 a yankin arewa maso yamma.

Wannan taki kamar yadda gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana kyauta ne ga manoma, kuma ɗaya daga cikin shirye-shiryen shugaban ƙasa ne na tallafawa harkar noma da manoma a Nijeriya

Haka kuma gwamnan jihar Katsina ɗin ya ƙara da cewa za su sanya ido su tabbatar takin zamanin ya kai inda ake so, ya kai, ta hanyar sa ido akan waɗanda aka ɗorawa alhakin tafiyar da wannan shiri.

Raɗɗa ya bayyana cewa wannan shiri na bada takin zamani kyauta an yi shi ne domin manoma na gaskiya wanda za a sanya ido don ganin abin ya kai gare su, ba tare da an karkatar da shi ba.

Dangane da ƙoƙarin gwamnatin tarayya na samar da takin zamani gwamna Raɗɗa ya ce jihar Katsina kawai ta samu buhu 20,160 wanda zata rabawa manoma 5,040 a ƙarƙashin shirin inganta harkokin noma a Nijeriya

Haka kuma ya bayyana wannan yunkuri na shugaban ƙasa a matsayin wani namijin ƙoƙari na farfaɗo da darajar noma musamman a arewacin Nijeriya da take da daɗaɗan tarihi a ɓangaren noma

To, sai dai kamar yadda masu sharhi akan al’amuran yau da kullum suka bayyana shi ne, yanzu matsalar manoma guda biyu ce, wato matsalar tsadar taki da kuma matsalolin ɓarayin daji wanda ake buƙatar kawo ƙarshen rashin tsaro fiye da komi a wannan lokaci.

Shin ina ƙaƙarin da gwamnatoci ke cewa suna yi akan sha’anin tsaro,? A iya cewa da yawan manoma ba su ganshi ba, domin matsalar na cigaba da ƙara zama ƙarfen ƙafa ga manoma da sauran al’umma. To yanzu ina mafita?

Ita dai wannan matsalar tsaron idan za a iya tunawa tuni ta raba da yawan al’umma daga garuruwan su, inda aka samu sasanshi ne tsakanin al’umma da ɓarayin daji sun fara komawa garuruwan su domin fuskantar wannan damina.

To, sai dai akwai wuraren da babu yadda za a yi al’umma su koma saboda yadda matsalar ta yi muni so sai, daman dai fatan da ake da shi shi ne, ganin an yi sasanshi kuma an fara ganin alfanun abin a wasu wurare yasa aka yi fatan cewa daminar bana za a yi noma so sai yadda ya kamata.

Daga yankunan da ake yin noma so sai a jihar Katsina yanzu haka an yanke masu sadarwa saboda matsalar tsaro sannan an hana su zuba fetur a cikin jarkoki wanda hakan na shafar yadda suke  tafiyar da  sha’anin noman na bana.

Kamar yadda aka bayyana gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina sun rabawa manoma kayan aiki ciki harda ƙaramar tarakta ta noma mai amfani da man fetur wanda yanzu samar da man fetur ɗin domin yin amfani zai kasance wani babban ƙalubale ga manoma.

A wani sabon yunkuri da aka ce gwamnatoci na yi domin ganin an dawo da zaman lafiya a yankunan da ke fama da matsanancin rashin tsaro wanda zai baiwa manoman yin noma ba tare da wata fargaba ba shi ne karin jami’an tsaro a jihar Katsina

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ce ya daɗe bai ga ƙarin jami’an tsaron da gwamnatin tarayya ta turo jihar Katsina ba kamar a wannan lokacin ba da suka haɗa da sojoji da ƴan sanda da jami’an hukumar DSS da sauran jami’an tsaro

A cewar sa, yana fatan wannan yunkuri zai taimaka wajen ganin an samu nasarar murkushe wannan matsala da taki ci yaƙi cinye wa shekara da shekaru wanda kuma ta yi sanadiyar lakume rayuka da dukiyoyi da ba a san adadin su ba.

Yanzu gwamna Raɗɗa na cigaba da tattaunawa da ɓangarori daban-daban domin laluɓo hanyar da za a magance wannan matsala, abin jira a gani shi ne, irin tasirin da wannan yunkuri na baya baya nan zai yi akan wannan iftila’i na ɓarayin daji masu satar jama’a da hana nona.

Katsina
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Katsina
El-Zaharadeen Umar
+ posts Bio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Wakilin Sin: Kar A Bari Sabon Nau’in Ra’ayin Nuna Karfin Soja Ya Haifar Da Karin Tasiri

Wakilin Sin: Kar A Bari Sabon Nau'in Ra'ayin Nuna Karfin Soja Ya Haifar Da Karin Tasiri

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.